29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

2023: IBB, Obasanjo, Saraki, da Secondus sun yi ganawar sirri

Labarai2023: IBB, Obasanjo, Saraki, da Secondus sun yi ganawar sirri

Yayin da zaben 2023 ke karatowa, jaridar Leadership ta ruwaito cewa tsohon shugaban mulkin soji Janar Ibrahim Badamasi Babangida, tsohon shugaban kasa olusegun Obasanjo da wasu manya manya daga cikin jam’iyar PDP sun yi wata ganawar sirri ranar Talata 17 ga watan Agusta a garin Minna, babban birnin jihar Neja.

Kamar yadda jaridar ta ruwaito, shugaban jam’iyar PDP ta kasa Prince Uche Secondus, tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki, gwamnan jihar Akwa Ibom Emmanuel Udom; tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi da kuma Sanata Ben Obi suna cikin tattaunawar.

2023

Jim kadan bayan Obasanjo ya isa garin Minna don halartar bikin cikar Babaangida shekaru 80 da haihuwa, ya jagoranci tawagar manyan mutanen zuwa wajen taron, wanda suka gabatar da shi cikin sirri.

An bayyana cewa Obasanjo ya isa gidan tsohon shugaban kasar dake kan dutse da misalin karfe 9 na safe, inda ya wuce kai tsaye wajen taron tare da sauran manyan mutanen irin su tsohon ministan tsaro, Janar Aliyu Gusau (Rtd) da Janar Aliyu Akilu (Rtd).

Wani wanda ke kusanci da wajen taron wanda ya bukaci a boye sunanshi, ya bayyana cewa:

Ba abin mamaki bane don sun hana ku ‘yan jaridaa shiga wajen taron. Sun san abinda za su yi, ku ‘yan jarida kuna hana su yin abinda ya kamata.

Idan ku ka duba ba wai iya ‘yan jarida suka hana shiga ba, hatta makusanta na IBB dake Minnaa suma an hana ssu shiga wajen. Wannan biki ya bawa manyan mutanen damar tattaunawa ne kawai.

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa akwai wani boyayyen abu dake faruwa a gidan tsohon shugaban kasar a lokacin bikin cikar tashi shekaru 80.

Rahoton ya bayyana cewa tun da safe misalin karfe 7, ‘yan uwa da abokanan arziki suka dingaa tururuwar shiga gidan don taya tsohon shugaban kasar murna.

Idan ba a manta ba a ‘yan kwanakin nan ne dai kungiyar kafafen sadarwa ta shugaba Buhari ta zargi wani tsohon shugaban kasar Najeriya da kokarin tilasta shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi murabus.

Kungiyar mai nu na goyon bayan Buhari ta yi wannan zargin ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta, Niyi Akinsiju, dda kuma sakataren kungiyarr, Cassidy Madueke, a babban birnin tarayya Abuja.

Kungiyar ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar da kuma wasu mutane da ba ta bayyana sunayensu ba sune ke da hannu a wannan yunkuri na tumbuke shugaba Buhari.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Leadership

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe