36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Kotu ta raba ma’aurata da suka shekara 32 tare bayan an gano mijin bai biya sadaki ba

LabaraiKotu ta raba ma'aurata da suka shekara 32 tare bayan an gano mijin bai biya sadaki ba
  • Wata kotu ta raba wasu ma’aurata da suka shekara 32 suna tare a matsayin mata da miji
  • Kotun ta raba auren ne bayan an gano cewa dama can mijin bai biya sadaki ba, amma kuma har sun haifi yara har guda biyar
  • Mijin ne ya fara kai karar matar gaban kotun akan ta dauke yaran ta gudu da su ba tare da ta sanar dashi ba

A ranar Laraba ne, wata kotu dake zaune a jihar Ekiti ta raba auren wasu ma’arauta masu suna Mr Oladipo Ogunleye da matarsa Adeola Falade wadanda suka shekara 32 suna zaune tare ba tare da mijin ya biya sadaki ba.

Alkalin kotun, Mrs Yemisi Ojo, ta raba auren ne saboda kama mijin da aka yi da laifin dukar matar.

Da take gabatar da shari’ar, alkalin kotun tace dama can babu wani aure dake tsakanin mutanen guda biyu. Inda a karshe ta bukaci kowannensu ya kama gabanshi.

“Ina shawartar matar da ta dinga barin yaran suna zuwa suna zama tare da mahaifinsu, domin su saba da juna.

KU KARANTA: Ana neman dan sanda ruwa a jallo bayan ya harbi budurwar shi da bindiga a baki

“Hak kuma kotu ta bukaci mutumin ya cigaba da daukar nauyin ‘ya’yansa ciki kuwa har da biya musu kudin makaranta. Haka kuma muna bukatar dukkansu su zauna lafiya,” a cewar ta, inda ta kara da cewa duk wanda a cikinsu ya saba wannan dokoki da kotu ta gindaya zai fuskanci fushin shari’a.

Kotu

Da farko dai, mutumin mai shekaru 61, wanda yake aikin kanikanci, ya bayyana cewa babu aure tsakaninshi da matar, amma kuma suna da ‘ya’ya har guda biyar.

Mutumin ya bayyanawa kotu cewa a lokacin da suke zaune tare, shine yake daukar nauyin komai na gidan ciki kuwa hadda kula da yaran, amma tun lokacin da matar ta gudu da yaran, sai ya daina wahala a kansu.

A karshe Ogunleye, ya roki kotun da ta kawo karshen dangantakar dake tsakaninsa da matar.

KU KARANTA: Da duminsa: Tsohon gwamnan Adamawa, ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC tare da dubunnan mutanensa

Falade mai shekaru 48, wacce take aikin gwamnati, ta karyata wannan zargi.

“Mijina yana duka na, sannan yana bina a lokuta da dama da gudu. Haka kuma yana yi mini barazanar korata daga gidan shi,” ta ce.

Ango ya saki Amaryar shi a wajen daurin aure, bayan an aika masa da hotunan tsiraicinta

An daura auren da aka rabu a wajen daurin aure sakamakon halayen banza da amaryar take da su a baya. Ma’auratan na cikin farin ciki da annushuwa a wajen bikinsu, sai aka bawa angon kyautar fure dauke da wani boyayyen sako.

Rubutun dake jikin takardar ya sanya mijin ya fara zargin halayen amaryar tashi, hakan ya sanya shi duba wasu hotuna da aka aiko masa da su.

Wannan hotuna dai tsohon saurayin amaryar shi ne ya aiko masa da su, inda da yawa daga cikinsu na tsiraici ne.

Hotunan sunyi muni matuka, hakan ya sanya angon fushi sosai, inda a wajen ya yanke shawarar kawo karshen auren na su baki daya.

Duk da cewa mutane na ta faman holewa a wajen bikin hakan bai hana shi fidda sanarwar cewa ya sake ta ba.

Daga baya amaryar ta fito ta fadi gaskiya, inda tace kwarai a baya sunyi soyayyya da tsohon saurayinta wacce ta kai ga sun aikata abubuwa marasa dadin ji, amma daga baya sun gano cewa ba za su iya zama tare ba, hakan ya sanya suka yanke shawarar rabuwa, kuma iyayenta suka samo mata wanda ta aura a lokacin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe