36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Amarya ta yiwa uwar mijinta dukan tsiya kan ta sawa auren su ido ta hana su zaman lafiya

LabaraiAmarya ta yiwa uwar mijinta dukan tsiya kan ta sawa auren su ido ta hana su zaman lafiya

Babu wanda zai taba tunanin cewa rikici zai haifar da zaman lafiya da aka shafe lokaci ana fama, sai dai kuma hakan ya zama masalaha bayan wata amarya ‘yar kasar Afrika ta Kudu ta yiwa surukarta dukan tsiya, sakamakon sa mata ido da ta yi akan aurensu da danta.

Bayan wani rubutu da wata mai suna @Theeladi ta wallafa a shafinta, ta bayyana cewa surukur ta ki daga wa ma’auratan kafa tun bayan auren su. Amaryar wacce take ‘yar uwace a wajen wacce ta wallafa rubutun, ta yanke shawarar yin dambe da uwar mijin nata.

Sun shafe shekaru suna rikicin uwar miji da mata

A cewar @TheeLadi, ‘yar uwarta da surukarta sun shafe shekaru suna samun sabani tsakaninsu, saboda suna zaune a gida daya, auren ‘yar uwartan babu dadin ji ko kadan.

An dan samu masalaha tsakanin matan na tsawon lokaci, sai dai kuma da uwar mijin ta taso da maganar cewa amaryar taki haihuwa, sannan za ta je ta samo mishi wata matar da za ta haifa masa ‘ya’ya.

Wannan magana ya sanya matar ta yiwa surukar dukan tsiya a lokacin da ya rage su biyu a gidan, sai dai kuma da aka tambayi dangane da dukan surukartan, ta musanta maganar.

Manyan Dalilan da su ke sa miskilan maza farin jini da tasiri a zuciyoyin ‘yan mata

Amaryar dama bata daukar raini ko kadan

Ga dai yadda lamarin ya faru, kamar yadda @TheeLadi ta wallafa a shafinta:

‘Yar uwata irin mutanen nan ne da basu da kunya, haka rayuwarta take, kuma muddin ka nemi ka shiga rayuwarta, to ka shirya jiran abinda zai biyo baya.

Misali akwai wani Kawun mu da ya yi kokarin dukan ta (a lokacin ina jin ba ta fi shekara 9 ba), saboda ta yi rashin kunya, ai kuwa a lokacin ta cewa Kawun mu, idan ya isa su yi dambe. Ita dama can haka rayuwarta take.

Sai dai kuma aure ya koya mata hankali, domin kuwa a koda yaushe cikin tashin hankali ta ke da surukarta. Mahaifin mijinta yana sanya baki a wasu lokutan, amma hakan baya canja komai.

Ba su jituwa ko kadan amma a haka suka cigaba da zama na hakuri da juna. Bayan shekaru masu yawa, sai Mamazala (uwar mijin) ta yi kokarin zagin ‘yar uwata akan cewa ba ta haihuwa, ta yi banza da ita a lokacin. Sai dai kuma da taji abin ya yi yawa. Sai ta sanarwa da mijinta ya yiwa mahaifiyarshi magana. Mijin ya yi mata magana, amma matsalar ba koda yaushe yake gida ba, yana aiki a kamfanin gine-gine. Hakan ya bawa mahaifiyarshi damar cigaba da zagin ‘yar uwata..

A hankali abin ta ya fara yawa, har taa fa ce mata za ta saka shi ya auro wata matar tunda ita juya ce ba ta haihuwa. A lokacin ran ‘yar uwata ya baci sosai, amma ta yi hakuri har mijinta ya dawo gida. A lokacin da mijin ya dawo gida, ita ta riga ta gama tattare kayanta ta gaya masa baza ta iya zama ana cigaba da zaginta ba.

Amaryar ta yiwa uwar mijin duka bayan mijin baya gida

Tsautsayi ya sanya mijin da mahaifinsa suka fita za su kai matar da aka ce za a auro mata gida, suka bar ‘yar uwata da surukarta a gida. A wajen suka fara zage-zage da cin mutuncin juna. Ai kuwa a lokacin ‘yar uwata ta yanke shawarar yi mata duka. Matar ta kasa rama dukan, kawai ta fara kuka.

Lokacin da mijin da Babanshi suka dawo, sai ta ce ya kai ta gidan iyayenta. Surukar ta ce tayi mata duka, ita kuma ta musanta wannan zance, ta ce ita ko kuda bata taba ba. Ta ce daga yaya za ta daki tsohuwa.

A karshe dai mijin ya samu aiki mai kyau ya kama hayar wani sabaon giida ya dawo da matarshi ciki suka cigaba da zama. Yanzu haka sun haifi yara hudu, ita ma kuma ta samu aikin yi. A yanzu haka dai kamar komai ya koma dai-dai tsakaninsu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe