27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Tirkashi: Abdulsalami Abubakar ya yiwa Igbo da Yarbawa dake son a raba Najeriya gargadi da kakkausar murya

LabaraiTirkashi: Abdulsalami Abubakar ya yiwa Igbo da Yarbawa dake son a raba Najeriya gargadi da kakkausar murya

Tsohon shugaban mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, ya aika da mummunan gargadi ga kabilar Igbo dake goyon bayan Nnamdi Kanu, da kuma Yarbawa dake goyon bayan Sunday Igboho, akan su yi watsi da soki burutsun da suke na son raba Najeriya.

Jaridar Daily Times ta ruwaito cewa, Abdulsalami ya bayyana hakane a Abuja ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, a lokacin taron da aka gabatar na Ibrahim Badamasi Babangida, wanda aka gabatar a dakin taro na Ibrahim da Maryam Babangida.

Jaridar Labarun Hausa ta gano cewa tsohon shugaban kasar ya ce sakamakon alaka dake tsakanin kabilu da kuma aure da kabilun suke da juna ba zai yiwu Najeriya ta rabu baa.

Abdulsalami ya bukaci ‘yan Najeriya suyi hakuri su rungumi kaddara, su kuma yi aiki tare don ganin an samu zaman lafiya da hadin kai.

Abdulsalami Abubakar

Ya ce:

Ko da ace an raba Najeriya yanzu, mai za ku yi? Yayin da duk inda ka shiga a Najeriya, za ka ga Bahaushe ya auri Bayarbiya, ko Igbo ya auri Itsekiri da dai sauran su.

Saboda haka idan kace za ka raba, ya zaka yi da wadannan ma’aurata, ya zaka sanya iyaka tsakaninsu? Hakan zai yi wahala sosai.

Abdulsalami Abubakar ya shawarci ‘yan Najeriya kan cewa sai an hadu an zama tsintsiya madaurinki daya wajen ganin an kawo karshen matsalar dake kasar, haka kuma ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su tona asirin masu kawo matsala a kasar ta rashin tsaro.

Haka kuma jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa, da yake magana akan matsalar tsaro dake addabar kasar, Abdulsalami Abubakar ya ce duka ‘yan ta’addar da suka hada da Boko Haram, masu garkuwa da mutane da sauran masu ayyuka na ta’addanci, duka suna zaune ne a cikin ‘yan Najeriya, inda ya ce tabbas mutane sun san su.

Ya ce:

Saboda haka, mu bayyanawa hukumomin tsaro ko su waye, kuma mu hada kan mu wajen kawo karshen matsalar tsaro.

Kar ku zabi dan takarar da ya wuce shekara 60 – IBB ya bayyana ‘Yan Najeriya wanda za su zaba shugaban kasa

Burin jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, dana tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na hawa kujerar shugaban kasar Najeriya ka iya zuwa da cikas a shekarar 2023.

Arise TV ta ruwaito cewa tsohon shugaban kasar mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya shawarci ‘yan Najeriya kada su yi tsautsayin zabar dan takarar da ya wuce shekara 60 a duniya a matsayin shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Jaridar Labarun Hausa ta gano cewa Atiku da Tinubu, wanda yake tsohon gwamnan jihar Legas daga shekarar 1999 zuwa 2007, zai cika shekara 70 a duniya a shekarar 2023.

Haka shi ma tsohon mataimakin shugaban kasar, wanda yake da shekaru 75 a wannan shekarar, zai kai shekara 77 a lokacin, inda shi kuma Tinubu a watan Maris din da ya gabata ya cika shekara 68, hakan na nuni da cewa zuwa 2023 shi ma zai kai shekara 70 a duniya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Daily Times

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe