34.1 C
Abuja
Wednesday, March 29, 2023

An hana mawakin da ya zagi Annabi a Kano ganin lauya

LabaraiAn hana mawakin da ya zagi Annabi a Kano ganin lauya

Mawakin nan dan shekara 22, mai suna Yahaya Sharif-Aminu, wanda kotun Shari’ar Musulunci ta jihar Kano ta yankewa hukuncin kisa a ranar 10 ga watan Agusta shekarar 2020, an hana shi ganin lauya duk da cewa kwanaki 30 da aka bashi ya daukaka kara zasu kare a ranar 9 ga watan Satumba.

Jaridar PUNCH ta gano cewa an hana mawakin daukaka karar, inda har gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa a shirye yake sanya hannu akan hukuncin da aka yanke masa da zarar kwanaki 30 da aka gindaya masa sun cika.

Da yake magana da wakilin jaridar PUNCH a ranar Juma’a, lauyan dake kare hakkin dan adam, Mr. Femi Falana (SAN), ya ce ya bukaci lauya yaje ya gana da Sharif-Aminu, amma an hana lauyan shiga cikin gidan yarin.

Ya ce: “Na tura lauya ya tsaya akan shari’ar da kuma ganawa da (Sharif-Aminu), amma an hana shi ganinshi.”

A kokarin hira da kakakin hukumar gidan yarin ta Najeriya, Austin Njoku, bai samu ba, yayin da yaki daga wayarshi, sannan kuma yaki dawo da marani a sakon da aka aika masa ranar Juma’a.

Mawakin wanda yake zaune a unguwar Sharifai a cikin jihar Kano, ana zargin shi da batanci ga Annabi Muhammad (SAW), a wata waka da yayi ta yadu a manhajar WhatsApp a watan Maris, 2020. Matasa dai sun kone gidansu baki daya, inda kuma suka gabatar da zanga-zanga akan ‘yan sanda, hukumar Hisbah ta yanke hukuncin kisa a kanshi.

Mawakin wanda ya gudu, an kamo shi, inda ake zargin shi da laifin sabawa sashi na 382 na kudin tsarin mulkin jihar Kano, wanda aka gindaya shi kan shari’ar Musulunci.

Wasu lauyoyi da yawa a jihar Kano sun sanar da jaridar PUNCH cewa akwai lauyoyi da yawa da suka ki yarda su tsayawa Sharif-Aminu, saboda yanayin abinda ka iya biyo baya a jihar ta Kano.

Lauyan ya ce: “Yawancin lauyoyin dana tambaya a jihar Kano da su tsaya mishi sunki yarda saboda tsoro. Da yawa suna tsoron za’a iya kone musu ofishinsu, ko kuma a kashe su saboda suna kare wanda yayi batanci. Saboda haka da yawa daga cikin lauyoyin suna goyon bayan hukuncin kisan da aka yankewa saurayin, kuma sun kasa komai a kai.

“Kuma tabbas idan aka zo magana da ta hada da addini, su kansu ‘yan sanda kansu daurewa yake yi su radsa abinda za su yi. Haka suma ‘yan siyasa sun kasa magana, saboda suna tsoron kada sunansu ya baci idan suka kare shi.

Kungiyar lauyoyi Musulmai ta Najeriya wacce take da karfi sosai a jihar da kuma sauran jihohin da ake koyi da shari’ar Musulunci, sun yankewa mawakin hukuncin kisa, inda suka bayyana hukunci yayi daidai kuma ya tafi daidai da dokar jihar.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo Labarun Hausa a shafukan sadarwar ku kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/laabarunhausa/

Twitter: https://www.twitter.com/labarunhausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye llabarunhausaa@gmail.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe