24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya mayarwa masu cewa ya yi murabus martani

LabaraiShugaban jam'iyyar PDP na kasa ya mayarwa masu cewa ya yi murabus martani

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, ya ce babu dalilin da zai saka ya sauka daga mukamin shi duk da irin matsin lamba da yake samu daga wajen wasu mambobin jam’iyyar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, shugaban jam’iyyar ya bukaci mutanen da suke so ya yi murabus din da su bayyana laifukan da ya aikata.

Labarun Hausa sun gano cewa Secondus ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ta bakin mataimakin shi a fannin sadarwa, Ike Abonyi.

Shugaban jam’iyyar ta PDP ya ce zai cigaba da zama a kujerar shi kuma ba zai fasa ayyukan da yake yi ba na kawo cigaba a jam’iyyar, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Sanarwar ta ce:

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus ya ce ba zai sauka daga mukamin shi ba.

Prince Secondus ya bayyana hakane a sanarwar da mai taimaka masa a fannin sadarwa ya fitar, inda ya bukaci tsirarun mutanen da suke so ya sauka da su fito su yi karara su bayyana laifin da ya aikata, da kuma dalilin da ya sa zai yi murabus.

Ya ce zai cigaba da aikin da ya sanya a gaba na jam’iyyar wanda ya dauki alkawari a lokacin da aka zabe shi a matsayin shugaban jam’iyyar watanni 44 da suka wuce.

Jam'iyyar PDP

Shugabannin jam’iyyar PDP da kungiyoyi da dama sun yi kira ga shugaban jam’iyyar Uche Secondus da ya sauka daga mukamin shi, musamman ma yanzu da jam’iyyar take rasa ‘ya’yanta da suke kaura suna komawa babbar jam’iyya mai mulki.

‘Yan Arewa sun bukaci shugaban jam’iyyar PDP na kasa yayi murabus ko su fice daga jam’iyyar

Rikicin dake faruwa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP na cigaba da ruruwa yayin da ‘yan Arewa dake cikin jam’iyyar suka bukaci shugaban jam’iyyar na kasa Uche Secondus da yayi murabus.

Kungiyar ta ‘yan arewan da suka bayyana cewa suna wakiltar ‘yan siyasa na jihohi 19 dake Arewacin Najeriya da Abuja, sun bukaci Secondus ya sauka don kare martabar jam’iyyar, da kuma ceto jam’iyyar daga rugujewa.

Jaridar The Sun, ta ruwaito cewa kungiyar ta bayyana hakane a wajen wani taro da ta gabatar a jihar Kaduna ranar Juma’a 6 ga watan Agusta, 2021.

Shugaban tsare-tsare na kungiyar, Yahaya Salisu, ya yi zargin cewa gazawar Secondus ce ta sanya jam’iyyar PDP ta rasa mambobi masu kishin ta, inda suka koma jam’iyya mai mulki ta APC.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: The Nation

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe