34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Wani mutumi ya zama shugaban makaranta, bayan shafe shekaru 25 yana share-share a makarantar

LabaraiWani mutumi ya zama shugaban makaranta, bayan shafe shekaru 25 yana share-share a makarantar

Wani mutumi ya tabbatarwa da duniya cewa aiki tukuru da hakuri na iya canja rayuwar mutum wata rana. Gabe Sonnier ya yi aikin share-share da goge-goge a makarantar firamare dake Port Barre na tsawon shekaru 25.

Wata rana a shekarar 1985, shugaban makarantar, Westley Jones, ya kira shi ya sanar dashi cewa zai fi so ace yaga yana rubutawa yara sakamakon jarrabawa da wannan share-share da yake yi, kamar dai yadda jaridar Goal Cast ta ruwaito.

Ya dauki hanyar samun sa’ar rayuwa

Gabe ya ce ya yi murna sosai da jin wannan magana daga bakin shugaban makarantar. A lokacin da yake shekaru 39, Gabe na zuwa makarantar yayi aikin share-sharen da ya saba sannan kuma ya yi aikin da shugaban makarantar ya bukaci ya yi.

Bayan ya samu takardar digiri a fannin koyarwa, ya samu aikin koyarwa a matsayin malamin makaranta a shekarar 2008 a makarantar Port Barre. Bai tsaya a nan ba, ya cigaba da karatu har ya samu takardar digiri na biyu. A shekarar 2013, an bawa Gabe mukamin shugaban makarantar baki daya, kamar yadda CBS ta ruwaito.

Ya cigaba da biyayya duk da wannan matsayi da ya samu

Wani abin ban sha’awa dangane da Gabe shine, duk da samun wannan matsayi da ya yi, har ya zuwa yau shine yake share ofishin sa ya goge, da yake bayani dangane da yadda ya kai wannan matsayi, Gabe ya ce:

Ka da ka bari halin da kake ciki a yanzu ya kashe maka guiwa akan abinda za ka zama a gobe. Na sha gaya musu ita rayuwar ba wai yadda ka fara ta bane, yadda ka gama ta shine abin dubawa.

Da N50,000 kacal na fara sana’a ta – Cewar miloniya da ya mallaki kamfanin mai a Dubai

Shugaban kamfanin man fetur na Total Grace Oil and Gas, Dr. Henry Bolaji Akinduro, ya bayyana cewa kamfanin shi da yanzu ke kawo masa miliyoyin nairori, ya fara shi da naira dubu hamsin (N50,000) kacal.

Kamfanin na Total Grace Oil and Gas, yana da helkwata a Hadaddiyar Daular Larabawa (Dubai), da gidajen mai guda biyar a Najeriya.

Da yake hira da wakilin Legit.ng, Adewinmi Adeoye, shugaban kamfanin ya bayyana cewa kudin da ya fara kasuwancin da shi ya karba daga makaranta ne a jihar Ondo, lokacin da yake karatu a kwalejin lafiya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe