24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

An bayyana Yemi Osinbajo a matsayin wanda zai gaji shugaba Buhari a 2023

LabaraiAn bayyana Yemi Osinbajo a matsayin wanda zai gaji shugaba Buhari a 2023

An bayyana mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a matsayin wanda yafi dacewa da ya maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2023.

Wata kungiya mai suna Osinbajo Grassroots Organization (OGO), ta bayyana mataimakin shugaban kasar a matsayin makoma ga cigaban Najeriya a shekarar 2023, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Shugaban kungiyar na kasa, Foluso Ojo, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya bayyana cewa kungiyar ta sanya ranar 8 ga watan Agusta a matsayin ranar taya Osinbajo murna.

Ya ce halayen shugabanci da mataimakin shugaban kasar ke da su ya nuna cewa zai iya maye gurbin shugaba Buhari a 2023, inda ya bayyana hakan a matsayin cigaba ga gwamnati mai ci.

Kungiyar ta ce;

Mun bayyana mataimakin shugaban kasa a matsayin jagora mai halaye na gari; wanda zai iya ci gaba da ayyukan alheri da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya riga ya fara,

Cewar Foluso Ojo

Kungiyar ta bayyana cewa Osinbajo yana da halaye da ake neman duk wani shugaba ya mallaka, sannan kuma yana da burin ganin ya kawo cigaba a Najeriya, jaridar The News ta ruwaito.

Kungiyar ta bayyana cewa za ta gabatar da wannan taro ne don ta jawo hankalin mataimakin shugaban kasar ya fito takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

A cewar shugaban kungiyar, za su gabatar da taron ta yanar gizo sannan kuma su yi wani a Abuja da kuma sauran jihohi 36 na fadin kasar, haka kuma za su bi dokokin da aka sanya na hana yaduwar annobar Coronavirus.

‘Yan Arewa sun bukaci shugaban jam’iyyar PDP na kasa yayi murabus ko su fice daga jam’iyyar

Rikicin dake faruwa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP na cigaba da ruruwa yayin da ‘yan Arewa dake cikin jam’iyyar suka bukaci shugaban jam’iyyar na kasa Uche Secondus da yayi murabus.

Kungiyar ta ‘yan arewan da suka bayyana cewa suna wakiltar ‘yan siyasa na jihohi 19 dake Arewacin Najeriya da Abuja, sun bukaci Secondus ya sauka don kare martabar jam’iyyar, da kuma ceto jam’iyyar daga rugujewa.

Jaridar The Sun, ta ruwaito cewa kungiyar ta bayyana hakane a wajen wani taro da ta gabatar a jihar Kaduna ranar Juma’a 6 ga watan Agusta, 2021.

Shugaban tsare-tsare na kungiyar, Yahaya Salisu, ya yi zargin cewa gazawar Secondus ce ta sanya jam’iyyar PDP ta rasa mambobi masu kishin ta, inda suka koma jam’iyya mai mulki ta APC.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: The Cable

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe