29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

‘Yan Arewa sun bukaci shugaban jam’iyyar PDP na kasa yayi murabus ko su fice daga jam’iyyar

Labarai'Yan Arewa sun bukaci shugaban jam'iyyar PDP na kasa yayi murabus ko su fice daga jam'iyyar

Rikicin dake faruwa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP na cigaba da ruruwa yayin da ‘yan Arewa dake cikin jam’iyyar suka bukaci shugaban jam’iyyar na kasa Uche Secondus da yayi murabus.

Kungiyar ta ‘yan arewan da suka bayyana cewa suna wakiltar ‘yan siyasa na jihohi 19 dake Arewacin Najeriya da Abuja, sun bukaci Secondus ya sauka don kare martabar jam’iyyar, da kuma ceto jam’iyyar daga rugujewa.

Jaridar The Sun, ta ruwaito cewa kungiyar ta bayyana hakane a wajen wani taro da ta gabatar a jihar Kaduna ranar Juma’a 6 ga watan Agusta, 2021.

Shugaban tsare-tsare na kungiyar, Yahaya Salisu, ya yi zargin cewa gazawar Secondus ce ta sanya jam’iyyar PDP ta rasa mambobi masu kishin ta, inda suka koma jam’iyya mai mulki ta APC.

Ya ce:

Muna kira ga shugaban jam’iyya na kasa, Uche Secondus da yayi murabus cikin gaggawa, donn kare jam’iyyar mu daga durkushewa, kamar yadda tuni mun riga mun rasa gwamnoni, ‘yan kwamitin amintattu, sanatoci, mambobin majalisar wakilai da dai sauran su, inda suka koma APC.

Kungiyar tayi barazanar cewa za ta tattaro ‘yan jam’iyyar su gabatar da zanga-zanga a gaban helkwatar jam’iyyar dake Abuja, matukar shugabannin jam’iyyar ba su sanya Secondus ya yi murabus ba.

Haka kuma Salisu ya bayyana cewa matukar Secondus bai sauka ba to duka za su tattare nasu ya nasu su bar jam’iyyar ta PDP.

Kwamitin Amintattu ta PDP taki yadda a tsige Secondus

A wani labari na daban kuma, kwamitin amintattu ta jam’iyyar PDP ta ki amincewa da shirin tsige Secondus da ake yi, inda suka ce a barshi ya kammala wa’adinsa.

Bugu da kari, kwamitin amintattun ta kuma yi watsi da kiraye -kirayen a kaddamar da majalisar zartarwa ta wucin gadi wacce za ta gudanar da harkokin jam’iyyar a yayin da ake cigaba da samun takaddamar cikin gida.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: The Sun

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe