29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

An nuna mini cewa APC za ta sha kaye a zaben 2023 – Fasto Elijah

LabaraiAn nuna mini cewa APC za ta sha kaye a zaben 2023 - Fasto Elijah

Babban Faston cocin INRI Evangelical, Elijah Ayodele, ya yi hasashen cewa babbar jam’iyya mai mulki ta (APC) za ta kashi a zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa faston ya bayyana cewa hasashen sa zai zama gaskiya matukar babbar jam’iyyar mai mulki ba ta kawo karshen matsalar tsaro da tattalin arzikin kasa ba.

Shugaban na Kiristoci ya shawarci jam’iyyar ta APC akan ta kawo gyara a tafiyar da take idan har tana so ta samu nasara a zaben da za a gabatar a shekarar ta 2023.

Faston ya kara da cewa a shekarar 2023 Talakawa za su tashi tsaye wajen tabbatar da cewa anyi adalci a zaben da za ayi.

Shugabar jam’iyyar APC kuma ‘yar takarar Sanata a Arewa ta koma jam’iyyar PDP

Tsohuwar ‘yar takarar kujerar Sanata a jihar Benue, Mimi Adzape-Orubibi, ta rubutu takardar ficewa daga babbar jam’iyya mai mulki wato APC.

A ranar Talata 3 ga watan Agusta ne, Adzape-Orubibi ta sanarwa jaridar The Sun cewar ta aikawa shugaban gundumar Kumakwagh, dake cikin karamar hukumar Kwande, Hon. Terwase Aheeve takardar cewa za ta bar jam’iyyar.

A cewar jigon ta jam’iyyar APC, ta yanke shawarar barin jam’iyyar ne sakamakon ganin yadda jam’iyyar ta hana ta tallata kudurinta na siyasa ga al’umma.

Ta yi nuni da yadda ake cigaba da samun matsalar tsaro, da kuma matsalar tattalin arziki a fadin Najeriya, ga kuma matsaloli na rikicin jam’iyya da ake cigaba da samu a APC.

Da take cigaba da bayani akan yadda ta yanke shawara, ta kara da cewa:

Ina da cikakkiyar fahimta dangane da ilimi na siyasa, kuma zan fi son jam’iyyar da take darjanta al’ummarta da basu muhimmanci.

Ba na jin haushin kowanne mutum, akan abinda suka yi a baya ko kuma suka kasa yi a lokacin da nake cikin jam’iyyar APC. Ina sanya al’umma ne kan gaba fiye da komai.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Legit.ng

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe