24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Yanzu-yanzu: Shugabar jam’iyyar APC kuma ‘yar takarar Sanata a Arewa ta koma jam’iyyar PDP

LabaraiYanzu-yanzu: Shugabar jam'iyyar APC kuma 'yar takarar Sanata a Arewa ta koma jam'iyyar PDP

Tsohuwar ‘yar takarar kujerar Sanata a jihar Benue, Mimi Adzape-Orubibi, ta rubutu takardar ficewa daga babbar jam’iyya mai mulki wato APC.

A ranar Talata 3 ga watan Agusta ne, Adzape-Orubibi ta sanarwa jaridar The Sun cewar ta aikawa shugaban gundumar Kumakwagh, dake cikin karamar hukumar Kwande, Hon. Terwase Aheeve takardar cewa za ta bar jam’iyyar.

Jam'iyyar APC

A cewar jigon ta jam’iyyar APC, ta yanke shawarar barin jam’iyyar ne sakamakon ganin yadda jam’iyyar ta hana ta tallata kudurinta na siyasa ga al’umma.

Ta yi nuni da yadda ake cigaba da samun matsalar tsaro, da kuma matsalar tattalin arziki a fadin Najeriya, ga kuma matsaloli na rikicin jam’iyya da ake cigaba da samu a APC.

Da take cigaba da bayani akan yadda ta yanke shawara, ta kara da cewa:

Ina da cikakkiyar fahimta dangane da ilimi na siyasa, kuma zan fi son jam’iyyar da take darjanta al’ummarta da basu muhimmanci.

Ba na jin haushin kowanne mutum, akan abinda suka yi a baya ko kuma suka kasa yi a lokacin da nake cikin jam’iyyar APC. Ina sanya al’umma ne kan gaba fiye da komai.

Tambuwal – Babu wani abu a duniya da zai sa na koma jam’iyyar APC

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya sanar da cewa babu wani abu a duniyar nan da zai saka ya koma jam’iyyar APC mai mulki.

Tambuwal ya bayyana haka a ranar Talata, 27 ga watan Yuli, a jihar Sokoto, a lokacin da yake caccakar jam’iyyar APC mai mulki akan yadda ta kasa cika alkawuran da ta yiwa ‘yan Najeriya.

Ya kara da cewa ‘yan Najeriya na cigaba da shan wahalar wannan gwamnatin mai mulki ta sanya su a ciki, kamar yadda jaridar Nigerian Tribune.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Legit.ng

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe