29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Gwamnatin tarayya za ta fara bawa talakawan da annobar COVID-19 ta shafa tallafin N50,000

LabaraiGwamnatin tarayya za ta fara bawa talakawan da annobar COVID-19 ta shafa tallafin N50,000

A cikin wannan watan ne gwamnatin tarayya za ta fara rabawa talakawa tsofaffi guda 200,000 da basu da ikon samun kudin shiga na rayuwar yau da kullum, kudade don rage radadin halin da annobar COVID-19 ta sanya su a ciki.

Gwamnatin tarayya ta bayyana hakane ta bakin mai kula da tsarin bayar da tallafin, wanda ke karkashin ma’aikatar ayyukan jin kai, Iorwa Apera, a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta, a wajen wani taro da aka gabatar a babban birnin Tarayya Abuja.

Ya ce za a fara aikawa mutanen da kudaden da zarar kwamitocin da aka dorawa alhakin tantance su sun kammala aikin su.

A cewar shi a kashi 4 daga cikin talakawa da marasa galihu miliyan 35, an yiwa mutum miliyan 8.5 rijista a cikin jihohi 36 dake fadin Najeriya, kamar yadda jaridar ThisDay ta ruwaito.

Ya kara da cewa mutane miliyann biyu, da aka ware su a matsayin tsofaffi, an same su ne ta hanyar amfani da wuraren da suke zama, shekarun su, matsayi, nakasa, da kuma ilimi.

Ministar kula da ayyukan jinkai, Sadiya Umar Farouk, a nata jawabin yayin ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bullo da wannan tsari ne don samar da cibiyar tsofafffin mutane ta kasa da kuma samar da hanyar jin matsalolin tsofaffin mutanen ke fuskanta a kasa.

Ta bayyana cewa matsalar yunwa, talauci game da annobar COVID-19 sune suka sanya gwamnatin tarayya ta yanke shawarar fitowa da wannan tsari don daidaita rayuwar marasa galihi a kasar.

Gwamnatin tarayya tayi alkawarin cigaba da bada tallafin N50,000 ga ‘yan Najeriya da annobar COVID-19 ta shafa

A kwanakin baya ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanke shawarar ba da damar cigaba da bayar da tallafin N50,000, a kokarin da yake na kawo saukin rayuwa ga ‘yan Najeriya, Channels TV ta ruwaito.

Kudin da gwamnatin tarayyar za ta fitar yana daga cikin kokarin da gwamnatin ke yi na rage tasirin annobar coronavirus akan ‘yan Najeriya, cewar Daily Times.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Legit.ng

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe