24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Yanzu-yanzu: Sama da mutu 50,000 sun canja sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a jihar Taraba

LabaraiYanzu-yanzu: Sama da mutu 50,000 sun canja sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC a jihar Taraba

Akalla mutum 50,000 ne a ranar Alhamis 29 ga watan Yuli, suka canja sheka daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP, da kuma jam’iyyar APGA suka koma jam’iyya mai mulki ta APC a jihar Taraba.

A rahoton da jaridar Daily Sun ta fitar, ta bayyana cewa daya daga cikin jigon jam’iyyar, Dalhatu Sangari, wanda ya karbi mutanen a garin Wukari, yace mutanen sun fito daga mazabu 52 dake yankin kudancin jihar.

Labarun Hausa sun gano cewa Sangari ya bayyana cewa wannan mutane ba karamin cigaba za su kawowa jam’iyyar ba a kokarin da take na kwace mulki a zabe mai zuwa.

Ya ce:

Dalilin da ya jawo canja shekar ba wani abu bane mai wahalar ganewa ba. Kowanne mutum mai hankali ya san cewa jam’iyyar PDP na gab da wargajewa. Inda jam’iyyar APC ta zama ita ce makoma. Mutanen da ke da hangen nesa ba sa bukatar a gaya musu hanyar da ya kamata su bi. Wannan dalili ne ya sanya mutane ke ta shigowa jam’iyyar mu a yanzu.

A cewar rahoton, daya daga cikin masu canja shekar Janar Adamu Tubase Ibrahim (Rtd) ya ce ya yanke shawarar shiga jam’iyyar APC ne daga jam’iyyar UDP, saboda a baya can shi dan jam’iyyar APC ne sai ya bar jam’iyyar saboda rashin adalci da aka yi musu.

Ya ce a matsayinsa na jagoran tafiyar Marigayiya Sanata Aisha Alhassan wanda ya bar jam’iyyar APC ya koma UDP, ya bar duk wani abu da yake tsohuwar jam’iyyar shi ya dawo APC domin ya taimaka mata ta cimma duka nasarorin da take buri a shekarar 2023.

Tambuwal – Babu wani abu a duniya da zai sa na koma jam’iyyar APC

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya sanar da cewa babu wani abu a duniyar nan da zai saka ya koma jam’iyyar APC mai mulki.

Tambuwal ya bayyana haka a ranar Talata, 27 ga watan Yuli, a jihar Sokoto, a lokacin da yake caccakar jam’iyyar APC mai mulki akan yadda ta kasa cika alkawuran da ta yiwa ‘yan Najeriya.

Ya kara da cewa ‘yan Najeriya na cigaba da shan wahalar wannan gwamnatin mai mulki ta sanya su a ciki, kamar yadda jaridar Nigerian Tribune.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Legit.ng

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe