29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

Hotuna: Abba Kyari tauraron dan sanda da mashahuran mutane ke hassada da shafinsa na Instagram

LabaraiHotuna: Abba Kyari tauraron dan sanda da mashahuran mutane ke hassada da shafinsa na Instagram

Kafin yanzu, sunan DCP Abba Kyari ya zama abin sha’awa da mutuntawa tsakanin ‘yan Najeriya, kuma sunan na sanya fargaba da tsoro a zuciyar masu cin amanar kasa, amma a cikin awanni 24, an alakanta sunanshi dana ‘yan damfara, sakamakon wani zargi da kotun Amurka ke yi akan shi kan damfarar fitaccen dan damfara Hushpuppi.

Hushpuppi, wanda ainahin sunanshi shine Ramon Abbas, ya bayyana cewa ya bawa Abba Kyari cin hanci, ya kama abokin harkar shi.

Sai dai kuma, fitaccen dan sandan ya karyata wannan zargi da Hushpuppi yake yi akan shi, inda ya ce bai karbi ko kobo daga wajen shi ba.

Jaridar Labarun Hausa ta ruwaito cewa kotun kasar Amurka ta bawa hukumar FBI umarnin kamo Abba Kyari biyo bayan zargin shi da ake da hannu a badakalar Hushpuppi.

Sai dai kumaa, a wani rahoto mai alaka da wannan din, Sufeto Janar, Usman Alkali Baba, ya bukaci a gabatar da bincike akan zargin da ake yiwa Abba Kyari.

Kyari dai yana da masoya 73,000 a shafinsa na Instagram a daidai lokacin da muke rubuta wannan rahoto, kuma mutane da dama na son mu’amala da shi.

Daga wallafa irin nasarorin da yake samu, zuwa wallafa hotunan abokanan shi da ‘yan uwanshi, Kyari yana wallafa kusan duk abubuwan da yake yi na rayuwa a shafinsa na Instagram.

Daya dagaa cikin hotunan shi da yafi yin suna a ‘yan kwanakin nan shine, wanda ya wallafa shi da Obi Cubana, fitaccen dan kasuwar nan na Abuja, wanda yayi suna sosai sakamakon kudi da aka dinga wasa dasu a lokacin bikin jana’izzar mahaifiyarsa, Uche Iyiegbu.

A cikin rubutun nashi da ya wallafa Kyari ya bayyana Cubana a matsayin dan kasuwa mai aiki tukuru da ya sani shekaru da dama a rayuwar sa.

Wasu daga cikin shahararrun mutane da ya wallafa hotunan shi tare da su, sun hada da Aisha Buhari, matar shugaban kasa; Adamu Mohammed, tsohon sufeto janar na ‘yan sanda; Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai na Najeriya; Babagana Zulumm, gwamnan jihar Borno; Innocent Idibia, fitaccen mawaki da aka fi sani da 2baba; Davido; Bob Manuel Udokwu, jarumin Nollywood, da dai sauran su.

A kasa dai ga wasu daga cikin manyan hotunan da ya wallafa a shafin nasa na Instagram:

Abba Kyari da 2face
Kyari da 2face
Screen Shot 2021 07 30 at 12.08.55 AM 768x490 2
Kyari da Bob-Manuel Udokwu
Screen Shot 2021 07 30 at 12.08.23 AM 1 768x491 1
Kyari da Femi Gbajabiamila
Screen Shot 2021 07 30 at 12.07.59 AM 768x489 1
Kyari da Adamu Moohammed – Tsohon Sufeto Janar
Screen Shot 2021 07 30 at 12.06.00 AM 768x488 1
Kyari da Babagana Zulum – Gwamnan Borno
Screen Shot 2021 07 29 at 10.06.24 PM 768x470 1
Kyari da Aisha Buhari
Screen Shot 2021 07 30 at 12.07.24 AM 1 768x491 1
Kyari da Davido
DCP KYARI8
Kyari da Obi Cubana
DCP KYARI5 768x680 1
Kyari da kyatuttukan da ya samu a ofishin sa
DCP KYARI1
Abba Kyari akan titin da aka sanyawa sunanshi

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: The Cable

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe