27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Uroosa Arshid – ‘Yar aikin kwana-kwana ta farko da ta fara sanya Hijabi a Birtaniya

LabaraiUroosa Arshid - 'Yar aikin kwana-kwana ta farko da ta fara sanya Hijabi a Birtaniya

Wata budurwa ‘yar shekara 27 a duniya mai suna Uroosa Arshid, an bayyana cewa ta zama mace ta farko ‘yar aikin kashe gobara da ta fara sanya Hijabi. Arshid ta ce babban burinta a rayuwa shine ta zama ‘yar aikin kwana-kwana duk da kuwa mutane na kushe aikin.

A wata hira da aka yi da ita, Arshid ta ce ta tuna lokacin da take makaranta, a lokacin bata wuce shekara 8 ba a duniya, wasu ‘yan aikin kashe gobara uku suka je makarantar ta, tun daga lokacin taji tana sha’awar aikin.

Uroosa Arshid mace ta farko da ta fara sanya Hijabi

Ta kara da cewa ‘yan aikin kwana-kwana na daya daga cikin mutanen da suka fi kowa ceton al’umma, hakan ya sanya ta shiga wannan aiki. Babban burinta shine ta ga tana taimakawa mutane, da kuma kare rayukan mutane.

Kimanin shekaru biyu da suka gabata, Arshid ta shiga aikin kwana-kwana a ma’aikatar kashe gobara ta Nottinghamshire.

A cewar ta, koyon aikin na da matukar wahala, kuma duka sai da ta koyi kowanne mataki. Hakan ya sanya ta samu nasara sosai a wannan fannni..

Aikin kwana-kwana ba wai iya kashe wuta bane kawai, yana da ka’idoji da yawa da mutum ya kamata ya bi, cewar Arshid.

Ta gano ita ce mace ta farko da ta fara sanya Hijabi a aikin

Wani babban abin mamaki ma shine, ta gano cewa ita ce mace ta farko da ta fara sanya Hijabi a cikin masu irin wannan aiki na ta, bayan ta shafe shekara daya tana aikin. A lokacin ana neman wata daga wani yanki na kasar wacce zata taimaka mata ta kuma bata shawarwari, amma ba a samu Musulma ko daya ba.

Wannan dalilin ne ya sanya aka bayyana cewa Arshid ita ce mace ta farko dake aikin kashe gobara wacce ta fara sanya Hijabi a kasar Birtaniya..

Arshid ta ce wannan aiki da take yi ya taimaka mata matuka, har ta samo Hijabi na masu aikin kashe gobara wanda take sanyawa a kasan takunkuminta na iska. Tana fatan za ta zama abin koyi a wajen mata Musulmai da za su dinga yin koyi da ita su shiga wannan aiki.

uroosa arshid 1 1024x576 1

Manajar masu aikin kashe gobarar ta West Bridgford, Ashley Fullard, ta ce ma’aikatan kashe gobara an jima ana yi musu wani irin kallo na daban.

Suna so su zama abin koyi a wajen da suke yin aiki, kuma samun mutane da suke da al’ada ta daban da kuma yare ko addini, zai taimaka matuka wajen cigaban aikin, hakan ya sanya muke ganin Arshid za ta taimaka matuka.

Duk da dai cewa Arshid na fama da matsala ta nuna wariya daga wajen abokanan aikinta, ta zama abin koyi sosai a wajen mata Musulmai masu tasowa sosai.

Balarabiya ta auri maza 2 lokaci daya a birnin Jeddah

A cewar majiyoyi da dama da kuma yadda rahoton ya zo, an ruwaito cewa mahaifin wata yarinya ya aurar da ita ga wani mutumi ba tare da wancan mijin ya sake ta ba. Haka kuma sun boye maganar auren daga wajen tsohon mijinta.

Daga yaya ta auri maza biyu?

A yadda rahoton ya bayyana, matar na zaune da mijinta na tsawon watanni biyu, kafin ya bar birnin Jeddah ya tafi wajen aiki, sai matar ta tafi wajen iyayenta ta cigaba da zama da su. Ma’auratan ne suka yanke wannan shawara a tsakaninsu.

A lokacin da mijinta ya yi nisa da ita, mahaifin matar ya aurar da ita ga wani mutumin daban, inda ya sanar da mijin cewa wannan shine aurenta na farko, sai dai daga baya ya gano cewa ba haka lamarin yake ba daga wajen matar, inda ta sanar dashi cewa tuni tana da miji.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Islamic Information

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe