27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Gwanda na mutu dana bari Fulani su zauna a jiha ta – Gwamnan Arewa

LabaraiGwanda na mutu dana bari Fulani su zauna a jiha ta - Gwamnan Arewa

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya zargi gwamnatin tarayya akan cigaba da samun matsalar tsaro da ake yi a fadin kasar, inda ya zarge su da nuna halin ko in kula.

Ortom ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 27 ga watan Yuli, a garin Makurdi, inda ya ce gwamnatin tana daa duk wani abu da ya kamata tayi amfani dashi wajen kawo karshen matsalolin kasar, rahoton AIT.

Ya nuna rashin jin dadi akan yadda matsalar tsaro ta raba mutane da dama a jihar shi, inda ya kira da wajen abincin Najeriya, ya kara da cewa har yanzu yawan mutanen dake mutuwa sakamakon matsalar fulani makiyaya na cigaba da kara yawa kamar yadda kididdiga ta nuna.

Gwamnan ya sha alwashin gwanda ya mutu da ya sake bari fulani makiyaya su zauna a cikin jihar shi.

Zan hana fulani zama a jihata

Ya ce:

Wadannan ‘yan ta’adda suna nuna kansu a shafukan sada zumunta, suna bayyana manufarsu ta korar mutane daga gidajensu su kwace filayensu su kuma kashe su.

Kuma suna nan sakamakon gwamnatin tarayya, amma a wurina, idan har suka zo, to a shirye nake in mutuu fiye da in mika filayena ga Fulani. Idan har Allah bai kare ni ba, bana bukatar taimako daga wajen kowa.

Abinda yasa jihar Benue ta yanke shawarar bawa Fulani wajen kiwo – Ortom

A wani rahoton kuma, Fulani makiyaya da suke da niyyar yin kiwo a jihar Benue, za a basu wajen kiwo.

Gwamnan jihar Samuel Ortom, shine ya bayyana haka a Abuja, a wajen bikin haihuwar tsohon jakadan Najeriya na kasar Mexico, Iyorwuese Hagher, wanda ya cika shekaru 72 a duniya.

Ortom ya samau wakilcin kwamishinan ilimi na jihar Benue, Dennis Ityavyar. Ya ce jita-jitar da ake yadawa akan cewa yana shirin yaki da Fulani ba gaskiya bane, inda ya kara da cewa tarihi ya nuna cewa mutanen jihar Benue suna zaman lafiya sosai da al’ummar Fulani.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Legit.ng

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe