27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Dan takarar gwamnan Kano ya dauki nauyin rashin lafiyar Sani Garba SK ya kuma bashi kyautar N150,000

LabaraiAl'adaDan takarar gwamnan Kano ya dauki nauyin rashin lafiyar Sani Garba SK ya kuma bashi kyautar N150,000

Kamar yadda kowa ya sani fitaccen jarumin wasan Hausan nan Sani Garba SK, da yayi fice wajen wasan barkwanci, na fama da rashin lafiya, wacce ya shafe tsawon lokaci a kwance.

A yanzu haka Allah ya karbi addu’ar da ake ta yi masa domin kuwa wani dan siyasa ya dauki nauyin rashin lafiyar shi.

Malam Inuwa Waya wanda ake kira da (Raba Gardama) shine ya dauki nauyin kula da rashin lafiyar da Sani Garba SK ya dade yana fama da ita.

An bayyana cewa tun bayan jin rashin lafiyar da Sani Garba SK ke fama da ita, ta sa Malam Inuwa Waya ya tako takanas ta Kano har gidan Sani Garba SK Dan Fado, inda ya duba shi ya kuma yi masa ihsanin alkhairi kuma, nan take ya dauki nauyin kulawa da lafiyarsa ba tare da wani bata lokaci ba.

Jin dadin hakane yasa ‘yan unguwa da shugabannin ‘yan wasann Hausa da abokanai suka yi ta godiya da nuna jin dadin su akan hakan tare da fatan alkhairi.

Ya ce:

Lokacin da na samu labarin cewa Sani SK bashi da lafiya, hankalina ya tashi matuka, saboda SK mutum ne da ya bada gudummawa sosai wajen gyara tarbiyar matasan mu.

A lokacin da muka fara harkar siyasa, Sani Garba SK ya bada gudummawa sosai a lokacin wakoki tare da su mawaki Adamu Nagudu.

Inuwa Waya
Malam Inuwa Waya, wanda ya dauki nauyin Sani Garba SK

Ya ce shima mutum ne mai kaunar abubuwan Kannywood, yana bibiyar su a shafukansu da dama na sada zumunta, irin su Instagram, Facebook, Youtube da sauran su, haka kuma ya ce Kannywood na daya daga cikin kungiyoyin da idan ya samu abinda yake so zai tafi da su.

Yasha alwashin bunkasa masana’antar baki daya idan ya samu ya hau mulki, saboda aa cewarshi masana’antar na da matukar muhimmanci ga rayuwar dan adam.

Ya ce:

Mutane irin su SK bai kamata ace dan suna rashin lafiya ba, kuma an san cewa likita zai iya duba su ya bada magani, amma ace an tsaya an zuba ido. Saboda haka dole ne mu tashi mu saka hannu don tabbattar da cewa mun taimaka kuma mun bada gudummawa wajen ganin ya samu lafiya.

Ni ba wai nazo dan na duba shi bane kawai, yanzu haka zamu yi masa addu’a wacce ita ce ginshiki, na biyu kuma gobe zamu aiko da likita ya duba shi, idan ta kama zamu kai shi asibiti to, idan ma kuma za ayi masa magani ne a gida, duka ni zan dauki nauyin wannan dawainiyar.

Na san cewa tun ya fara rashin lafiyar nan bai samu ya fita ba, kuma na san cewa akwai dawainiya da yawa a kanshi ta iyali, saboda haka na bashi kyautar naira dubu dari da hamsin, don ayi cefanen gida ya kuma cigaba da kula da lafiyar sa.

Malam Inuwa Waya

A karshe ya bayyana cewa ya yiwa Ganduje bayani akan rashin lafiyar ta Sani SK, inda gwamnan yayi masa addu’a kuma ya mika sakon gaisuwar shi gare shi.

A nashi bayanin daya daga cikin aminai na Sani SK, Lawan Garba Taura, wanda yake shi ma daya ne daga cikin manyan jaruman Kannywood, yayi godiya ga Malam Inuwa Waya akan wannan ziyara da ya kai ta dubiyar babban abokin su, haka kuma yayi masa fatan alkhairi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Tashar Tsakar Gida

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe