24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Wani bawan Allah ya bude wurin cin abinci kyauta ga marasa galihu

LabaraiAl'adaWani bawan Allah ya bude wurin cin abinci kyauta ga marasa galihu

Wani mutumi mai suna, Derrick Walton, wanda a baya ya taba shiga hali na wahalar rayuwa da ya sanya ko wajen kwana bashi da shi, ya gwangwaje mutane marasa galihu.

Mutumin ya bude wurin cin abinci wanda mutane marasa galihu ke zuwa a kowacce ranar Litinin, suke cin abinci kyauta. Ya ce irin wadannan mutane na shiga wani hali, inda suke zaune cikin kadaici, da rashin masoya kusa da su.

Wani ya kara mini kwarin gwiwa a gidan dafa abinci

Mutumin ya ce a baya yayi abubuwa marasa kyau, inda ya shiga harkar shaye-shaye, ya zama baya iya rayuwa ba tare da ya sha kayan maye ba.

A cewar Derrick, rayuwar shi ta canja a lokacin da wani manajan wajen cin abinci ya yarda dashi ya bashi aikin yi. Kafin wannan aikii nashi yasha zuwa neman aiki aka kore shi.

Yadda ya yi ya samu aikin yi kuwa, shine:

Gab da ina kokarin fidda rai da rayuwa, a ranar 10 ga wata, ba zan taba mancewa ba, naje gidan abincin Girka a cikin garin Detroit. Na gana da wani mutumi, na gaya masa, “Kaga na yi abubuwa marasa kyau a rayuwa ta, bana neman kudi kyauta, abinda nake so shine ka bani dama, ni kuma na tabbata ba zan taba baka kunya ba.”

Derrick

Samun nasara a rayuwa babu sauki

Duk da na bayyana a wajen cikin kaya masu datti, mutumin ya bashi dama ya gwada basirar shi. Ya zage dantse yayi aiki tukuru, inda ya yi ta tara kudi har ya samu ya bude shagon sayar da Pizza.

Abinci

A kowacce ranar Litinin, Derrick yana rufe shagon shi ga masu sayen abincin shi, sai ya budewa marasa galihu su shiga su ci abinci kala-kala kyauta.

Mutane da dama sun shiga wannan abu da yake yi domin taimakawa, inda a kowanne mako suke samar da mota da take bi lungu daa sako tana rabawa mutane abinci.

A wani labari makamancin haka, wani mutumi shi ma mai tausayi mai suna Brian Birkett, ya sha alwashin kare rayuwar shi wajen tabbatar da cewa mutane marasa galihu sun samu abincin ci.

A kowanne mako, mutumin wanda yake karbar kudin fansho, yana dafa abinci ya rabawa mutane 50 da ya samu akan titi. Abincin akwai shinkafa, dankali da kaza a ciki.

Banda wannan abinci da yake rabawa mutane wanda yake biya da kudin shi, ya kuma shiga kungiyar NGO, inda suke taimakawa wajen jin dadin al’umma.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Legit.ng

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe