24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Tausayi ya sa an budewa matar da take aikin tura ruwa a baro shagon sayar da kaya

LabaraiAl'adaTausayi ya sa an budewa matar da take aikin tura ruwa a baro shagon sayar da kaya

Mutanen kasar Kenya sun nuna halin su na kulawa da taimako, bayan sun taimakawa wata mata da aka nuno tana aikin sayar da ruwa a baro a garin Dagoretti, na jihar Nairobi dake kasar ta Kenya.

Hoton matar mai suna Everlyn Ndinyuka, tana tura katuwar baro cike da jarkokin ruwa ya sanya tausayi sosai a cikin al’ummar yankin, musamman ma wata mai son taimako mai suna Wanja Mwaura wacce ta taimaka mata.

Ta cika burin ta

Ndinyuka ta bayyanawa Wanja cewa ita babban burinta shine ta bude shagon sayar da kayan abinci, ai kuwa Wanja wacce dama halayyarta ce taimakawa masu karamin karfi, ta cikawa matar nan burinta.

A ranar Alhamis 22 ga watan Yuli ne dai Wanja ta wallafa wani rubutu a shafinta na Facebook, inda take bayyana cewa sun budewa Ndinyuka shago.

Ndunyika matar da take aikin garuwa

Wanja ta ce:

Ina fatan kun tuna da Mama Dennis, matar da take aikin garuwa, wacce take tura jarka 20 ta ruwa? Mun samu mun taimaka mata ta bude shago wanda take burin samu da jimawa.

Yanzu haka tana kokari taga ta daidaita komai a shagon.

Wanja Mwaura

Haka kuma Wanja ta wallafa hotuna a shafinta na Facebook a lokacin da ta kaiwa Ndinyuka taimakon wasu jakankunan kayan sayarwa.

Ku Karanta: Ana ta yabon budurwa ‘yar shekara 18 da take wankin babbar mota don ta dauki nauyin karatun ta

Wannan abu ya yiwa Ndinyuka dadi matuka, hakan ya sanya ta nuna godiyar ta, ta ce:

Ina godiya matuka ga wadanda suka hada ni da Wanja har ta samu ta taimake ni. Allah ya albarkaci gidajen ku. Ban san yadda zan gode muku ba a gaskiyar magana.

Everlyn Ndinyuka
Wanja Mwaura

An biya mata kudin hayar gidan ta

Wanja ta kuma bayyana cewa sun biyawa Ndinyuka kudin haya na tsawon watanni hudu, kafin su yi mata fatan alkhairi su wuce.

Ina yi muku godiya kwarai da gaske ‘yan uwana na Facebook. Ina fatan za ta mai da kai wajen ganin wannan kasuwanci ya bunkasa, tunda dama shine babban burinta a rayuwa.

Wanja Mwaura

Mutane sun sanya albarka

Mutane da dama a kasar Kenya sun ji dadin wannan abu da ya faru, inda suka dinga rubuta sharhi suna cewa:

Abu yayi kyau sosai

Linda Kalya

Allah ubangiji ya taimake ki da Mama Dennis

Mumbi Bruce

Ki cigaba da aikin alkhairi.

Wairimu Marie

Aikin ki yayi kyau ‘yar uwata.

Eriss Khajira

Ki gaya mana inda take sana’arta saboda wadanda suke zaune a yankin ta su taimaka mata.

Sparky Chelsea Gall

Takaitaccen labarin Ndinyuka

A ranar 10 ga watan Yuni ne dai Wanja ta wallafa hoton Ndinyuka tana tura ruwa a baro, inda ta bukaci a sanar da ita yankin da take zaune.

Bayan kwana hudu, Wanja ta samu ta kai mata ziyara, sai ta gano cewa Ndinyuka na zaune a daki daya ne tare da ‘ya’yanta guda biyar, inda yanzu haka an dauki nauyin biyu daga cikin su.

Wanja ta ce wannan aiki na tura baro da matar take yi ya sanya taji tana so ta taimaka mata.

Wannan abu da take yi ya riga ya kashe mata jiki. Sakamon aikin ya sanya tana ciwon baya da kafa. Mu taimaka mu ceto rayuwar ta, ko dan darajar yaran da take da su, wadanda suke jira sai ta samo ta ba su.

Wanja Mwaura

Hadi Usman dattijo mai shekaru 67 da ya kirkiro murhu mai amfani da ruwa da baya bukatar gas ko kalanzir

Wani hazikin dattijo dan Najeriya da ke zaune a unguwar Jeka da fari da ke jihar Gombe ya kawowa jama’a sauki inda ya yi kokarin kirkirar sabon samfurin murhun dafa abinci, wanda ya ke amfani da ruwa, Hadi Usman mai shekara 67 da haihuwa, ya kirkiri murhun girki wanda baya bukatar amfani da gas ko kalanzir wajen kunna shi.

Dalilin da yasa ya kirkiri wanan murhu mai aiki da ruwa

Kamfanin dillancin labarai na PR Nigeria ya ruwaito cewa, dattijon wanda yake makeri ne ya kirkiro wanan fasaha ne saboda burinsa na son bayar da tallafin wajen ganin an samu saukin rayuwa.

Wani faifan bidiyo na YouTube wanda kafafen yada labarai suka yada ya nuna yanda Malam Hadi Usman yake bayani kan yadda ake amfani da murhun.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Legit.ng

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe