27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Ana ta yabon budurwa ‘yar shekara 18 da take wankin babbar mota don ta dauki nauyin karatun ta

LabaraiAna ta yabon budurwa 'yar shekara 18 da take wankin babbar mota don ta dauki nauyin karatun ta

Yayin da dalibai da yawan gaske suke fadawa sana’o’i daban daban domin samun kudin kashewa da kuma wanda zasu dauki nauyin karatun su, yanayin yadda wata matashiyar budurwa ta dauki sana’arta ya bawa mutane da yawa sha’awa.

Yarinyar ‘yar shekara 18 mai suna Chinyere, ta dauki aikin wankin babbar motar ruwa (tanka) a matsayin aikinn da za ta dauki nauyin karatun ta da shi.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Instagram mai suna @mufasatundeednut, an nuno jajircacciyar budurwar da bokiti cike da ruwa da kuma sabulu yayin da take wanke tayar motar da soson wankin mota.

Da aka yi hira da ita akan yadda take aikin ta a ranar Lahadi da ta gabata, Chinyere ta ce, wasu lokutan takan wanke motoci uku inda ake ba ta 30 GHc, kimanin naira 2,100 a kudin Najeriya.

Mutane na ta tofa albarkacin bakin su kan bidiyon

Jarumar mace, zan so ace na samu lambar iyayenta, tana bukatar mu kara mata kwarin guiwa

@nwadibia_1

Don Allah ina so na taimakawa wannan karamar yarinyar, shin akwai wanda zai iya hadani da ita?

@amyyoungkelly

Shin yaushe za ta gama wanke wannan tankar? Allah ka sani mutane na wahala a wannan kasar.

@jaycruisee

Ban san mai yasa wannan labari yayi mini kama da labarin da aka kirkira ba, duba hannunta wanda za ta yi amfani dashi ta wanke tanka, wani lokacin ma har guda uku. Gaskiya wannan labari akwai alamar tambaya.

@bee_chalin

Budurwa da take aikin buga bulo don ta biyawa kanta kudin makaranta ta kammala karatun ta

Wata budurwa da aka bayyana sunanta da Sharon Mbabazi an taya ta murna a shafukan sadarwa yayin da ta kammala karatu daga jami’ar Mutesa Royal, bayan ta dauki nauyin kanta ta hanyar aikin buga bulo.

A wani rubutu da wani mutumi mai suna Elphas Saizi ya wallafa a shafinsa na LinkedIn, ya bayyana cewa budurwar ‘yar kasar Uganda ta kammala karatun ta na digiri a fannin sadarwa, ta kuma nunawa duniya cewa zage dantse na taimakawa wajen samun nasara.

A cewar Elphas, Sharon ta rasa mahaifiyarta a lokacin tana yarinya ‘yar shekara biyar a duniya, inda a maimakon ta koma bara ko ta zauna sai wani ya kawo ya bata sai ta fara aikin buga bulo, inda a nan take samun kudin da take rayuwa da shi.

Matashi dan shekara 16 ya canjawa kekensa fasali zuwa babur ta hanyar amfani da injin janareto

Adewale matashin yaro ne dan shekara 16 mai matukar fasaha ta kere-kere, inda ya canjawa kekensa fasali daga keke ya mayar da shi babur ta hanyar amfani da injin janareto na wuta. Ya ce ya kashe naira dubu talatin (30000) da kuma goyon baya da ya samu daga wajen mahaifin shi yayin da mutane ke yi masa dariya…

Yaro dan shekara 16, Adewale Quoyim, shaida ne akan yadda wani tunanin fikirar kirkira na mutum zai iya bada bankaye. Ya canja kekensa zuwa babur, da tunanin sa shi kadai.

Da yake magana da BBC bangaren turancin pidgin, a wata tattaunawa, yace, mutane sunyi ta gaya masa cewa ba zai iya canja injin janareto ya koma aiki kamar babur ba.

Mahaifinsa ya karfafa masa gwiwa

Yayin da abinda mutane ke fada ke neman rage masa kwarin gwiwa, sai mahaifinsa ya kara zaburar dashi. Bayan ya kammala aikin har yana hawan kayansa sai kuma mutanen da suke ganin ba zai iya ba, suka koma suna mamaki gami da murna.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe