36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Yadda aka yi Sallah lafiya aka gama lafiya, ya zama shaida ga ‘yan Najeriya cewa matsalar tsaro ta kusa zuwa karshe – Fadar Shugaban Kasa

LabaraiYadda aka yi Sallah lafiya aka gama lafiya, ya zama shaida ga 'yan Najeriya cewa matsalar tsaro ta kusa zuwa karshe - Fadar Shugaban Kasa

A wani rahoto da jaridar Daily Nigerian ta fitar ta ruwaito cewa fadar shugaban kasa ta bayyana cewa babu wani harin bindiga ko na bam da ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga suka kai har aka gabatar da bikin babbar sallah aka gama.

Mai bawa shugaban kasa shawara ta musamman a fannin sadarwa, Femi Adesina, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar wacce aka sanyawa sunaa “Allah ya albarkaci rundunonin mu”.

A sanarwar da, Mr Adesina ya fitar, ya tabbatar da cewa halin da ake ciki na rashin tsaro a Najeriya zai zo karshe nan ba da dadewa ba.

‘Yan Najeriya za su ga karshen ta’addanci, matsalar tsaro, kashe-kashe, rashin kwanciyar hankali, garkuwa da mutane da sauran su. Zaman lafiya zai dawo kasar nan kamar ba a taba samun matsalar tsaro ba.

Haka kuma a ‘yan kwanakin nan, kun ji tashin bam ko kashe-kashe a lokacin bikin babbar sallah da aka yi a fadin kasar nan? a’a

Tabbas muna samun cigaba. Mun kusa kawo karshen lamarin. Allah zai kare rundunonin mu na yaki.

Mai bawa shugaban kasa shawara a fannin sadarwa – Femi Adesina
Buhari a lokacin sallah a Daura

Mr Adesina ya roki ‘yan Najeriya da su taya sojojin Najeriya da suke a filin daga da addu’a akan masu tada kayar baya da kuma ‘yan ta’adda da suke a fadin kasar nan.

Bindiga kawai ba za ta iya kawo karshen ‘yan ta’adda ba – Goodluck Jonathan

A wani rahoto da muka kawo muku kuma, ya nuna yadda tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya shawarci gwamnatin tarayya tayi amfani da fasahar zamani domin duba ga matsalar ‘yan bindiga da kuma sauran ayyuka na ta’addanci da ake fama da su a kasar nan.

Goodluck Jonathan ya bayar da shawarar ne a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuli, a lokacin bikin murnar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Osita Chidoka, na cika shekaru 50 a duniya, wanda aka gabatar a babban birnin tarayya Abuja, rahoton The Sun.

Tsohon shugaban kasar ya ce bindiga da sauran abubuwan yaki kadai baza su iya hana ‘yan ta’adda da barayi daina abinda suke yi ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Goodluck Jonathan ya yi bayanin cewa kasashe na samun cigaba ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Daily Nigerian

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe