29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Tabbas Abduljabbar bashi da lafiya, amma ban ce guba aka saka masa ba – Inji Lauyan sa

LabaraiAl'adaTabbas Abduljabbar bashi da lafiya, amma ban ce guba aka saka masa ba - Inji Lauyan sa

Bayan rikita zancen rashin lafiyar Abduljabbar da aka yi, zancen ya zama wani abu mai wahalar fahimta, inda wasu ke ganin cewa kamar dai akwai lauje cikin nadi.

Bayan rahoton da jaridar Daily Trust ta fitar na cewa bashi da lafiya yana zubar da jini ta duburar shi, sai wasu suka yada cewa ai guba aka saka masa a gidan yari, inda hakan ya tilasta hukumar gidan yari fitowa ta musanta wannan magana.

Sai dai kuma lafazin mai magana da yawun gidan gyaran halin yace, Abduljabbar na nan cikin koshin lafiya, kuma baya cin abincin gidan yarin, hasalima daga gidan sa ake kawo masa abincin da yake ci.

Mutane sun canja maganar lauyan

Wannan kalma ta yana cikin koshin lafiya ta taimaka sosai wajen kore wancan tsohon labarin da lauyan Abduljabbar, Barista Rabi’u Shu’aibu ya fadawa jaridar Daily Trust, hakan ya sanya ake ganin cewa babu abinda ya samu Malamin.

Daga baya dai lauyan Malamin, ya sake fitowa ya tabbatar da cewar tabbas Malamin bashi da lafiya, sai dai kuma ya bayyana cewa bai san a ina aka samo labarin cewa an saka masa guba ba, inda kalma ta saka guba din ita ce ta birkita zancen.

A takaice dai Abduljabbar yana fama da rashin lafiya, kuma yana zubar da jini kamar dai yadda lauyan nashi ya bayyanawa jaridar Daily Trust da, sai dai kuma babu wanda ya ce guba aka saka masa.

Abduljabbar Nasiru Kabara

Abduljabbar ya bayyana dalilin da yasa ya tuba ya kuma janye tuban sa dab da za a kama shi

A yammacin ranar Asabar ne hukumar ‘yan sanda suka yi awon gaba da Malam Abduljabbar Nasiru Kabara, inda kai tsaye aka mika shi kotun shari’ar addinin Musulunci dake kofar kudu, daga nan alkali ya iza keyar sa zuwa gidan gyaran hali, inda ya bayyana za a cigaba da zaman shari’arsa ranar 28 ga watan nan.

Sai dai ana dab da za a kama shin, jaridar Daily Trust sun samu damar tattaunawa da Malamin, inda ya amsa tambayoyin da suka yi masa, wanda a hirar ya tabbatar musu da ba gudu ba ja da baya akan da’awar da ya fara sai yaga abin da ya turewa buzu nadi.

Mukabalar da muka yi wasan kwaikwayo ce

A hirar da yayi da Daily Trust Abduljabbar ya tabbatar da cewa, mukabalar da suka yi wasan kwaikwayo ce da aka shirya aka kuma tsara komai tun kafin a zo gurin.

Ya ce duk wasu tsare-tsare da ya san da su an canja su kafin ya zo gurin, ya kara da cewa an tsara za ayi komai a bude da ga baya anyi a rurrufe ance za’a ba ni damar nada daga baya an canja, ance za a gayyato alkalai daga bangarori hudu daga baya aka kawo gida daya kawai, inda daga baya ma muka gano daga bangaren wadanda suke tuhumata yake, kuma shine wanda yafi tsanani a cikin su, haka aka bashi alkalin mukabalar to taya za ace anyi adalci?

Ya kara da cewa a tarihin duniya ban taba jin inda aka yi mukabala irin haka ba, an bada minti biyar ga mai tambaya, minti goma ga mai bada amsa, an kuma bayar da minti biyar ga mai yanke hukunci, yayi bayani.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Tashar Tsakar Gida

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe