24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Umoja: Kauyen da mata suka hana maza zama a cikin shi

LabaraiAl'adaUmoja: Kauyen da mata suka hana maza zama a cikin shi

A cikin tsakiyar Sahara can cikin kasar Kenya, an kirkiri wani kauye mai suna Umoja, wannan kauye mata ne zalla suka kirkire shi,

A kasar Kenya, akwai wata mata da tayi namijin kokari, ta kirkiri kauye guda sukutum, na mata kawai, wanda basa bari namiji ya shiga.

Shin wacece wannan mata, kuma daga ya ya ta kirkiri wannan kauye, sannan kuma mai yasa ba a bari maza su shiga?

A kasar Kenya, tsakiyar Sahara, akwai wani kauye mai suna Umoja, inda wata mata mai suan Rebecca ta jagoranci gina shi da kuma tafiyar da harkokin cikin kauyen.

Rebecca da ta kirkiri kauyen Umoja

Wannan mata mai suna Rebecca ita ce ta samar da wannan kauye. Shekaru 30 da suka gabata, Rebecca na cikin tashin hankali, sakamakon auren da tayi, mijinta na dukanta da cin zarafin ta.

Sai dai kuma a lokacin da tayi duba da kyau, ta ga cewa ba ita kadai bace ke cikin wannan hali, ma’ana ba komai bane a wannan yankin nasu don an kama mace anyi mata fyade, haka kuma ba komai bane a yiwa mata kanana aure ba tare da son su ba.

A lokacin da Rebecca ta bukaci shugabanninsu akan su kare su daga mazajensu da suke dukan su, babu wanda ya taimaka musu, kowa ya juya musu baya.

  • inspired 2015 08 samburu umoja kenya women village getty main
  • 534832039
  • 3777274613 1ea2de23dd o
  • 3777278631 175eeecd88 o
  • 3778078892 4d47c18630 o

Ku Karanta: Abubuwan mamaki game da wasu kasashen duniya

Wata rana ita da wasu mata guda 14 sun yanke shawarar gina kauyensu. Mazajensu sunyi ta yi musu dariya,
inda suke ganin baza su taba samun nasara ba, saboda suna ganin mata ne, kuma mata suna da rauni, sai dai kuma Rebecca da mutanen ta sun nuna musu ba haka lamarin yake ba.

Sun yanki fili, suka sanya masa suna UMOJA, inda hakan ke nufin ‘Hadin Kai’. Matan sunyi amfani da hannayensu suka gina gidajensu.

Suna hada abubuwan kwalliya na hannu dana wuya suna sayarwa da mutane da suka kai musu ziyarar bude ido.

Bayan haka kuma sun gina makaranta da suke koyar da ‘ya’yansu karatu. A wannan kauyen mata na rawa da waka cikin nishadi.

Yara maza na iya zama a wajen, amma da sun cika shekara 18 za a basu zabi akan su cigaba da zama idan sun amince za su bi dokokin su, ko kuma su fita su bar garin.

Da farko dai mazajensu sun cika da kishi, hakan ya sanya suka yi gini a kusa da nasu kauyen, domin su hana masu kai musu ziyara shiga.

Wani lokacin har shiga cikin kauyen suke suna kaiwa matan hari, sai dai Rebecca da mutanen ta suna da jarumta sosai.

Suka dinga tara kudi a hankali, suka saye kauyen mazan baki daya. A yanzu haka kauyen Umoja na dauke da mata guda 100, kuma kowacce a cikinsu na da labari mai ban tausayi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe