24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Budurwa da take aikin buga bulo don ta biyawa kanta kudin makaranta ta kammala karatun ta – Hotuna

LabaraiBudurwa da take aikin buga bulo don ta biyawa kanta kudin makaranta ta kammala karatun ta - Hotuna

Wata budurwa da aka bayyana sunanta da Sharon Mbabazi an taya ta murna a shafukan sadarwa yayin da ta kammala karatu daga jami’ar Mutesa Royal, bayan ta dauki nauyin kanta ta hanyar aikin buga bulo.

A wani rubutu da wani mutumi mai suna Elphas Saizi ya wallafa a shafinsa na LinkedIn, ya bayyana cewa budurwar ‘yar kasar Uganda ta kammala karatun ta na digiri a fannin sadarwa, ta kuma nunawa duniya cewa zage dantse na taimakawa wajen samun nasara.

Mahaifiyar budurwar ta rasu tana ‘yar shekara biyar

A cewar Elphas, Sharon ta rasa mahaifiyarta a lokacin tana yarinya ‘yar shekara biyar a duniya, inda a maimakon ta koma bara ko ta zauna sai wani ya kawo ya bata sai ta fara aikin buga bulo, inda a nan take samun kudin da take rayuwa da shi.

Ta zama abin misali na cewa yin aiki tukuru na taimakawa matuka wajen samun nasara. Kwarai kuwa akwai wani boyayyen abu dangane da zage dantse.

Ku Karanta: Mutane na ta tofa albarkacin bakinsu bayan wani babban Fasto yayi bikin Sallah a Masallaci tare da Musulmai

Elphas ya wallafa hotuna biyu na budurwar. Daya a ciki ta dauka a lokacin da take aikin buga bulo, dayan kuma ya nuno ta a cikin kayan da ta sanya lokacin da ta kammala karatu a jami’a. Yadda aka dauke ta cikin jin dadi a daya hoton yayi nuni da cewa wahalar da ta sha a baya tayi amfani.

Budurwa ta biya kanta kudin makaranta da aikin buga bulo

Ga murna da wasu ke taya budurwa Sharon

Babu abinda baya yiwuwa a rayuwa

Oladimeji Ige

Ina taya ki murna Sharon

Richard Ssesanga

Ina ganin hatta lokacin da take aikin buga bulo din, tana samun cigaba, kowacce hanya sa’a ce a ka idan har kana son abinda kake yi, zan iya bada shawara akan karatu, amma ba wai shine hanya ta samun cigaba ba.

Ntsako Emmah Mogatosi

Saurayi ya kirkiri kamfanin kanshi, shekaru kadan bayan budurwar shi ta guje shi bayan an kore shi a aiki

Wani matashin saurayi dan Najeriya ya burge masu amfani da shafukan sadarwa akan yadda lokaci daya Allah ya albarkaci rayuwar shi, bayan ya fuskanci matsaloli irin na rayuwa.

Saurayin mai suna Victor Anangwe ya hau shafin sadarwa na LinkedIn, ya wallafa yadda yayi kokarin hakura da komai na rayuwa a shekarar 2017 sakamakon rasa aikin shi da yayi.

Victor ya ce a wancan lokacin budurwar shi ta guje shi, inda ya rame sosai sakamakon hakan. Da yake wallafa hoton shi a shekarar 2017, saurayin ya ce ya rame daga 72kg zuwa 53kg.

Sabuwar rayuwa ga Victor

Allah ya daukaka shi a lokacin da ya fara tallar gidaje da na’ura mai kwakwalwa ta abokin aikin shi, inda a lokacin mahaifiyar shi ce ta taimaka masa da kudin da ya sayi data yake hawa.

A yau Victor, Allah ya taimake shi, abubuwa suna tafiya dai-dai a kamfaninsa mai suna Kareps.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe