24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Yanzu-yanzu: An kama Sunday Igboho a Cotonou yayin da yake shirin guduwa Turai

LabaraiYanzu-yanzu: An kama Sunday Igboho a Cotonou yayin da yake shirin guduwa Turai

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya shiga hannun jami’an tsaro.

Jaridar ta bayyana cewa an kama shi ne a filin jirgin sama dake Cotonou, cikin Jamhuriyar Benin, daya daga cikin kasashen dake makwabtaka da Najeriya a yankin Afrika ta yamma, a ranar Litinin da daddare.

Kama shi da jami’an tsaron suka yi a jamhuriyar Benin ya biyo bayan bayyanawa da hukumar ‘yan sandan farin kaya tayi DSS, na cewa tana neman shi ruwa a jallo.

Ana zargin shi da ajiye makamai ba bisa ka’ida ba, zargin da shi kuma musanta kenan.

Haka kuma jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa Sunday Igboho ya gama shiri tsaf domin gudawa kasar Jamus, inda ya dauki niyyar bi ta Cotonou.

Ku Karanta: ‘Yan jam’iyyar PDP na Arewa sun bayyana wanda za su tsayar takarar shugaban kasa a 2023

Miyetti Allah na zargin gwamnonin Kudu maso Yamma da boye Sunday Igboho

Idan ba a manta ba an zargi gwamnonin kudu maso yamma da boye Sunday Igboho wanda ake nema ruwa a jallo, a lokacin da hukumar DSS ke bincike akan inda yake..

Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, daya daga cikin manyan kungiyoyin Fulani dake Najeriya ita ce tayi wannan zargi, a wata hira da aka yi da mai magana da yawun kungiyar, Saleh Alhassann, inda suka zargi cewa gwamnonin kudu maso yamma guda shida sune suka boye Sunday Igboho.

Abubuwan da Sunday Igbboho ke yi siyasa ce

A cewar Alhassan, ana amfani da Igboho ne, inda yace duk abubuwan da yake yi siyasa ce. Ya ce duk da gwamnonin sun boye shi, tabbas jami’an tsaro za su nemo shi. A karshe ya bukaci gwamnonin, wadanda sune iyayen gidan na Igboho da su fito da shi don ya fuskanci shari’a.

Afenifere sun yi magana kan binciken da jami’an tsaro suka yi a gidan Igboho

A wani rahoto dake da alaka da wannan, kungiyar Afenifere, daya daga cikin kungiyoyin siyasa na Yarabawa, sunyi Allah wadai da binciken da aka yi a gidann Igboho.

A wata sanarwa da ta fitar ta bakin mai magana da yawun kungiyar, Jare Ajayi, kungiyar ta ce wannan abu da aka yiwa Sunday Igboho, na nuni da cewa Najeriya tana shirin komawa irin mulkin Marigayi Sani Abacha, inda ake kaiwa masu kalubalantar gwamnati hari.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da kada ta cutar da Sunday Igboho ko wani mutum daban idan har basu karya dokar kasa ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Legit.ng

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe