34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Balarabiya ta auri maza 2 lokaci daya a birnin Jeddah

LabaraiAl'adaBalarabiya ta auri maza 2 lokaci daya a birnin Jeddah

A cewar majiyoyi da dama da kuma yadda rahoton ya zo, an ruwaito cewa mahaifin wata yarinya ya aurar da ita ga wani mutumi ba tare da wancan mijin ya sake ta ba. Haka kuma sun boye maganar auren daga wajen tsohon mijinta.

Daga yaya ta auri maza biyu?

A yadda rahoton ya bayyana, matar na zaune da mijinta na tsawon watanni biyu, kafin ya bar birnin Jeddah ya tafi wajen aiki, sai matar ta tafi wajen iyayenta ta cigaba da zama da su. Ma’auratan ne suka yanke wannan shawara a tsakaninsu.

A lokacin da mijinta ya yi nisa da ita, mahaifin matar ya aurar da ita ga wani mutumin daban, inda ya sanar da mijin cewa wannan shine aurenta na farko, sai dai daga baya ya gano cewa ba haka lamarin yake ba daga wajen matar, inda ta sanar dashi cewa tuni tana da miji.

Mijin farkon ya samu labarin auren matar shin

A lokacin da tsohon mijin ya samu labarin cewa ta auri wani, sai yayi kokari ya samu yayi magana da sabon mijin matar shin, domin ya ji gaskiyar maganar, sannan kuma ya sanar dashi cewa shi bai saki matar shi ba.

Ku Karanta: Wuraren ban al’ajabi guda 7 a duniya

Duka mazajen sun shiga wani hali marar dadi, duka sai suka kai mahaifin matar kara kotu.

Mata ta auri maza 2

Bayanin da mahaifin matar ya yi

Bayan gabatar da bincike, mahaifin matar yayi bayani domin wanke kanshi. Ya ce, mijin ‘yar shi na farko ya sake ta, amma ya manta bai rubuta mata takarda ba sakamakon matsalar rashin kudi da suke fama dashi.

Ya kara da cewa akwai matsalar rashin kudi a tsakanin ma’auratan, sai dai mijin kuma ya karyata wannan magana ta shi.

A karshe kotu ta yanke hukuncin hukunta mahaifin matar saboda saba dokar addinin Musulunci da kuma cin mutuncin aure.

Amarya ta yiwa uwar mijinta dukan tsiya kan ta sawa auren su ido

Babu wanda zai taba tunanin cewa rikici zai haifar da zaman lafiya da aka shafe lokaci ana fama, sai dai kuma hakan ya zama masalaha bayan wata mata ‘yar kasar Afrika ta Kudu ta yiwa surukarta dukan tsiya, sakamakon sa mata ido da ta yi akan aurensu da danta.

Bayan wani rubutu da wata mai suna @Theeladi ta wallafa a shafinta, ta bayyana cewa surukur ta ki daga wa ma’auratan kafa tun bayan auren su. Amaryar wacce take ‘yar uwace a wajen wacce ta wallafa rubutun, ta yanke shawarar yin dambe da uwar mijin nata.

A cewar @TheeLadi, ‘yar uwarta da surukarta sun shafe shekaru suna samun sabani tsakaninsu, saboda suna zaune a gida daya, auren ‘yar uwartan babu dadin ji ko kadan.

An dan samu masalaha tsakanin matan na tsawon lokaci, sai dai kuma da uwar mijin ta taso da maganar cewa amaryar taki haihuwa, sannan za ta je ta samo mishi wata matar da za ta haifa masa ‘ya’ya.

https://www.labarunhausa.com/4571/amarya-ta-yiwa-uwar-mijinta-dukan-tsiya-kan-ta-sawa-auren-su-ido/

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe