34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Goodluck Jonathan: Bindiga kawai ba za ta iya kawo karshen ‘yan bindiga ba

LabaraiGoodluck Jonathan: Bindiga kawai ba za ta iya kawo karshen 'yan bindiga ba

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya shawarci gwamnatin tarayya tayi amfani da fasahar zamani domin duba ga matsalar ‘yan bindiga da kuma sauran ayyuka na ta’addanci da ake fama da su a kasar.

Goodluck Jonathan ya bayar da shawarar ne a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuli, a lokacin bikin murnar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Ossitaa Chidoka, na cika shekaru 50 a duniya, wanda aka gabatar a babban birnin tarayya Abuja, rahoton The Sun.

Tsohon shugaban kasar ya ce bindiga da sauran abubuwan yaki kadai baza su iya hana ‘yan bindiga da barayi daina abinda suke yi ba.

Goodluck Jonathan ya ce bindiga ba ita mafita ba wajen yaki da ‘yan bindiga

Matsalolin ta’addanci da fashi da makami dake faruwa a kasar nan ya nuna cewa bindiga kawai ba za ta iya dakatar da su ba.

Muna bukatar tsare-tsare daga gwamnatin tarayya, da kuma fasahar zamani, muna bukatar abubuwa da dama don dakatar da matsalar tsaro, ciki kuwaa hadda cin hanci daa muke maganar shi a koda yaushe, saboda ba zai yiwu kawai mu sanya doka ba kuma muyi tunanin dokar da kanta za ta kawo matsalar abinda muke ciki.

Ku Karanta: Buhari ya umarci gwamnonin Arewa guda 7 su kawo karshen matsalar tsaro a jihohin su

Daily Trust ta ruwaito cewa, tsohon shugaban kasar ya yi bayanin cewa kasashe na samun cigaba ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Goodluck Jonathan

‘Yan bindiga sun yiwa ‘yan sanda kwantan bauna a Zamfara

A wani rahoton kuma, wani kwanton bauna da ‘yan bindiga suka yiwa ‘yan sanda a jihar Zamfara yayi sanadiyyar mutuwar ‘yan sanda 13 a jihar.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da kashe ‘yan sanda 13 a wata sanarwa da kakakin rundunar, Mohammed Shehu ya fitar.

Shehu ya ce ‘yaan bindigar sun kai harin kauyen Kurar Mota, dake cikin karamar hukumar Bungudu a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuli, da misalin karfe 12:30 na rana.

‘Yan bindiga sun kai hari kauyukan Zamfara

A wani rahoto, ‘yan bindiga da suke goyon bayan, fitaccen dan bindiga mai suna Turji, sunyi kan mai uwa da wabi wajen kama ‘yan kauyuka da kuma matafiya a yankin karamar hukumar Shinnkafi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan kama mutane da ‘yan bindigar suka yi ya biyo bayan kama mahaifin shugaban su Turji da aka yi. Sun fara kai harin a ranar Juma’a 16 ga watan Yuli, inda suka yi garkuwa da kimanin mutum 150.

An ruwaito cewa an kama mahaifin Turji a Kano, kimanin mako biyu a suka wuce..

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Legit.ng

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe