24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Saurayi da budurwar shi ta guje shi bayan an kore shi a aiki, ya mallaki kamfanin kanshi

LabaraiAl'adaSaurayi da budurwar shi ta guje shi bayan an kore shi a aiki, ya mallaki kamfanin kanshi

Wani matashin saurayi dan Najeriya ya burge masu amfani da shafukan sadarwa akan yadda lokaci daya Allah ya albarkaci rayuwar shi, bayan ya fuskanci matsaloli irin na rayuwa.

Saurayin mai suna Victor Anangwe ya hau shafin sadarwa na LinkedIn, ya wallafa yadda yayi kokarin hakura da komai na rayuwa a shekarar 2017 sakamakon rasa aikin shi da yayi.

Victor ya ce a wancan lokacin budurwar shi ta guje shi, inda ya rame sosai sakamakon hakan. Da yake wallafa hoton shi a shekarar 2017, saurayin ya ce ya rame daga 72kg zuwa 53kg.

Sabuwar rayuwa ga Victor

Allah ya daukaka shi a lokacin da ya fara tallar gidaje da na’ura mai kwakwalwa ta abokin aikin shi, inda a lokacin mahaifiyar shi ce ta taimaka masa da kudin da ya sayi data yake hawa.

A yau Victor, Allah ya taimake shi, abubuwa suna tafiya dai-dai a kamfaninsa mai suna Kareps.

Saurayi

‘Yan Najeriya suna yi masa jinjina

Allah yana amfani da wata dama wani lokacin ya tilasta mutum ya fita ya nema, sannan kuma ya kori mutanen da bai kamata su kusance ka ba.

Hellen G.

Wannan babban darasi ne dan uwa, yanke kauna da rayuwa ba mafita ba ce. Muna farin ciki ganin cewa Allah yana taimaka maka… Sannan kuma ya zancen budurwar ka, tambaya ce kawai?

Jackson Njoroge

Ku Karanta: Na dauki aniyar gogawa maza 2000 cutar kanjamau – Budurwa

Wannan abin burgewa ne. Nima ina neman aiki ne, wani lokacin ina tambayar kai na, sai kuma na gano cewa ni mutum ce mai lafiya, karfi da kuma basira. Na san cewa lokacina na nan zuwa, wahala ta dan wani lokaci ce, kuma tana faruwa bisa wani dalili.

Nelly Resian

Ba ka kammala bamu labarin baki daya ba

Shugaban kamfanin Bwana, shin budurwar ka tayi kokarin dawowa, ko kuwa ta samu wani wanda take ganin ya fika maiko ne?

Ina yi maka murna dai da har ka yarda da kan ka, da kuma kaunar abinda kake yi.

Sai dai kuma ka cire wajen da budurwar kan ta juya maka baya a labarin a lokacin da lamari suka canja maka.

Muna so muji wannan labari nan gaba.

Francis Otieno

Saurayi ya yaudari budurwarsa bayan ta bashi kodar ta guda 1 an dasa ya samu sauki

Colleen Le budurwa ‘yar shekara 30, wadda take zaune a kasar Amurka, ta bayyana cewa saurayinta a wani lokaci a baya ya bukaci ayi masa dashen koda, saboda yana fama da ciwon koda mai tsanani, wanda ya sanya ake yi masa wankin kodar yana dan shekara 17.

Ta amince ta sadaukar masa da warin kodarta bayan likitoci sun tabbatar da cewa zata yi daidai da ta shi. Bayan an gama aikin ya samu lafiya, ‘yan watanni kadan sai ya ci amanarta ya gudu ya barta.

Colleen wacce take tauraruwar tiktok, ta sami dumbin masu sharhi a kan bidiyon ta da ta wallafa, wanda ta nuna jerin abubuwan rashin kyautawa da yayi mata, inda da yawa suka dinga yaba mata saboda ceto ransa da tayi kuma suna nuna ma bata dace da shi ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Legit.ng

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe