27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Abduljabbar ya bayyana dalilin da yasa ya tuba ya kuma janye tuban sa dab da za a kama shi

LabaraiAbduljabbar ya bayyana dalilin da yasa ya tuba ya kuma janye tuban sa dab da za a kama shi

A yammacin jiya ne hukumar ‘yan sanda suka yi awon gaba da Malam Abduljabbar Nasiru Kabara, inda kai tsaye aka mika shi kotun shari’ar addinin Musulunci dake kofar kudu, daga nan alkali ya iza keyar sa zuwa gidan gyaran hali, inda ya bayyana za a cigaba da zaman shari’arsa ranar 28 ga watan nan.

Sai dai a jiyan dab da za a kama shin, jaridar Daily Trust sun samu damar tattaunawa da Malamin, inda ya amsa tambayoyin da suka yi masa, wanda a hirar ya tabbatar musu da ba gudu ba ja da baya akan da’awar da ya fara sai yaga abin da ya turewa buzu nadi.

Mukabalar da muka yi wasan kwaikwayo ce

A hirar da yayi da Daily Trust Abduljabbar ya tabbatar da cewa, mukabalar da suka yi wasan kwaikwayo ce da aka shirya aka kuma tsara komai tun kafin a zo gurin.

Ya ce duk wasu tsare-tsare da ya san da su an canja su kafin ya zo gurin, ya kara da cewa an tsara za ayi komai a bude da ga baya anyi a rurrufe ance za’a ba ni damar nada daga baya an canja, ance za a gayyato alkalai daga bangarori hudu daga baya aka kawo gida daya kawai, inda daga baya ma muka gano daga bangaren wadanda suke tuhumata yake, kuma shine wanda yafi tsanani a cikin su, haka aka bashi alkalin mukabalar to taya za ace anyi adalci?

Ya kara da cewa a tarihin duniya ban taba jin inda aka yi mukabala irin haka ba, an bada minti biyar ga mai tambaya, minti goma ga mai bada amsa, an kuma bayar da minti biyar ga mai yanke hukunci, yayi bayani.

Ku Karanta: Da zanyi ido 2 da Abduljabbar sai na yi shahada na shake shi ya mutu – Jaruma Inteesar

Bayan haka kuma shi alkalin tun daga farko har karshen mukabalar kalubalanta ta yake yana kuma goyon bayan abokan mukabala ta a takaice ma yafi masu kalubalantar tawa zafafawa, wanda sai bayan mukabalar na samu gamsassun hujjoji na hotuna da bidiyo da suka tabbatar da a bangaren su yake ko wallafar shi da yayi a Facebook zai tabbatar da haka.

Na tuba ne domin a zauna lafiya

Da aka tambaye shi game da sautin murya da aka ji shi yana neman afuwa da janye kalaman sa bayan mukabalar, sai Abduljabbar ya ce, bayan an hanani damar bayyanawa mutane inda na samo wannan fatawa tawa yadda za su fahimta, sai mutane suka fusata suka dauka wadannan zantuka daga ni suke kawai.

Ya cigaba da cewa hakan ya sanya lamari ya tsananta mutane sukai kololuwar fusata, wasu basu san ya lamarin yake ba, kawai gani na su kai a zaune ana min tambayoyi ina bada amsar babu isasshen lokaci, hakan ya sanya suka yanke cewa kawai zantuka na ne na kirkiro.

Abduljabbar

Wannan ya sanya mutanen gari suka fusata gari ya yamutse sai makusanta na suka shawarce ni , suka ce tunda tilasta musu aka yi suka mini mummunar fahimta, suna so na fita na janye kalamai na domin hankali ya kwanta.

Ina so a sake shirya mukabala idan na samu nasara a kotu

Abduljabbar ya kara da cewa fatan shi shine idan Allah yasa suka yi nasara a kotu a sake hada wata mukabalar, inda za a bashi cikakkiyar damar da zai tabbatarwa mutane wadannan zantuka suna cikin littatafan nan ba daga wajen shi suka fito ba.

Ya ce ya janye kalaman shi ne kawai ba dan komai ba sai domin a zauna lafiya.

A karshe Abduljabbar ya bayyana sakon sa ga Malamai cewa su fahimci cewa shi addinin abu ne na hujja babu yadda za ayi ka canja fahimtar wani.

‘Yan Shi’a su sama da miliyan 300 ne, amma duk basu yadda da litattafan ku ba

Ya ce akwai wasu bangarori na addini da suma basu yadda da wadannan littafan ba, misali ‘Yan Shi’a sun fi mutum miliyan 300 a duniya, kuma basu yadda da wadannan litattafan ba, kuma hakan bai hana su zama Musulmai ba, haka kuma Kur’aniyyun.

Amma ya ce idan aka tambaye shi mai yasa baya shiru da bakinsa ba, ya kan bada amsa da tayaya zasu amsa wadannan mas’aloli ga kafirai, kowa ya san da wannan lamarin amma ba wanda yake magana a kai.

Bayan kammala mukabala ana jiran aji matakin da gwamnati za ta dauka kan wannan lamari da kuma janye kalamai da tuban da yayi, sai kuma aka ji shi yana cigaba da karatun sa a shafukan sada zumunta da nufin bada amsoshin mukabalar da aka yi, sai dai kuma jiya sai ga sanarwar ‘yan sanda sunyi awon gaba da shi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Tashar Tsakar Gida

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe