34.1 C
Abuja
Wednesday, March 29, 2023

Da zanyi ido 2 da Abduljabbar sai na yi shahada na shake shi ya mutu – Jaruma Inteesar

LabaraiAl'adaDa zanyi ido 2 da Abduljabbar sai na yi shahada na shake shi ya mutu - Jaruma Inteesar

Tsohuwar jaruma a Kannywood Inteesar Abdulkadir Adam wacce ta bayyana ficewar ta daga masana’antar shekarar da ta gabata ta yi wani bidiyo a shafinta na TikTok cikin bacin rai da kunar zuciya kan batancin da Abduljabbar yayi, da kuma yadda daliban sa ke yawo da hoton sa a cikin kwaryar birnin Kano ba tare da anyi komai a kai ba.

Idan na ga Abduljabbar zan shake shi mu mutu tare

Inteesar ta kara da cewa da za ta ganshi za tayi shahada ta shake shi ya mutu kowa ya huta.

Yanzu kusan wata biyu ko uku yana rayuwa a cikin garin Kanon da muka sani wacce ake yiwa kirari da Kano ta Dabo Tumbin Giwa Yaro ko da mai kazo an fika.

Yawanci duk wani da zai taso irin wannan a Kano ne, Alhamdulillah muna da manyan Malamai masu ilimi, muna da masu wayewa, muna da kowa da kowa.

Kwarai ilimi ne da hangen nesa na manyan mu yasa har suka ce a bashi dama ayi wata mukabala, amma ni a gani na da zanga mutumin nan babu abinda zai hana ni nayi jihadi na shake shi mu mutu tare.

Wai har a samu wasu mutane su dauki hotonshi su fito suna yawo a cikin gari suna kida suna waka, suna daga hoton tsinanne suna tafiya, hadda ma basu kariyar dan sanda guda daya. Wannan babban abin kunya ne wallahi.

Ni na dauka a cikin iyalanshi za a samu wanda zai shake shi ya murde kanshi cikin dare ya mutu.

Inteesar
Abduljabbar tsinanne ne - cewar Inteesar

KU KARANTA: Sarkin Kano ga Buhari – ‘Yan Najeriya na cikin matsananciyar yunwa

Wata ta ce Abduljabbar cikakken masoyin Annabi ne

Ba ta jima da wallafa wannan bidiyo ba sai aka fara yi mata tsokaci cikin masu tsokacin har da wata mai suna fateemerh19 tayi mata tsokaci da cewa:

Ke kince baki ji ba bama za kiji bba kenan baki da hujja duk wanda yace yayi batanci ga Manzon Allah karya yake domin shi cikakken masoyin annabi ne.

Ai kuwa take Inteesar ta sake yin wani bidiyon don yin martani ga fateemerh199 da cewa:

Ke baiwar Allah ni kuwa nake da hujja, saboda ko ban ji ba, iya abinda ake yi tashin hankalin da ake ciki ya isa ya sanar da mutum halin da ake ciki.

Ke ko iyayenki aka zaga, zaki zo kina maimaitawa ne ko kuma zaki zo kice sai kinji kwakwaf? Balantana Manzon Allah (SAW).

Ta yaya zanji cin mutuncin da aka yiwa Manzon Allah, ko iyayena aka zaga bazan je nace zan saurara naji ba.

Inda bai yi ba mai yasa bai yi musu ba, ya karyata abinda aka ce akan shi ba?

Ke iya abubuwan da mutane suke fada a shafukan sadarwa ya isa ya sanar dake girman abinda aka aikata.

Inteesar
137062612 5939815776053497 8706618019873187512 n

Baya ga wannan wani mai suna golden_c shima ya yi mata martani da cewa:

Gaskiya ke jaka ce, Malam Abduljabbar dinne tsinanne, gaskiya ke jahila ce.

Sai dai shi ma bata kyale shi ba, ta wanke shi tas a wani bidiyo da tayi a kanshi.

To yanzu tsakani da Allah akwai jaki kamar ka bawan Allah? Mutumin da yayi batanci ga Manzon Allah, sannan har ya jira abin yake ta yawo a shafukan sadarwa bai fito ya wanke kanshi ko ya nemi gafara ba.

Ya fito yayi magana ne saboda ya rasa yadda zai yi, saboda yaga cewa an kure shi, ni banji tausayin shi ba duk da wasu na cewa suna tausayin shi.

Inteesar

Ga bidiyon yadda lamarin ya kasance

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Tashar Tsakar Gida

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe