‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su ka lamushe wiwi mai nauyin 200kg bayan sun kwace ta a hannun ‘yan ta’adda inda su ka ajiye ta a caji ofis, LIB ta ruwaito.
Kotu ta saurari yadda berayen su ka lamushe wiwin da aka ajiye a matsayin shaida.
A wata takardar wacce aka karanta wa kotu, ta bayyana cewa:
“Beraye kananun dabbobi ne wadanda ba sa tsoron ‘yan sanda. Kuma abu mai wahala ne a boye wiwin daga wurinsu.”
Alkali Sanjay Chaudhary ya ce a wata takardar kotu, ‘yan sanda su gabatar da wiwi mai nauyin 195kg da su ka kwace a matsayin shaida, inda su ka ce beraye sun shanye ta.
A wata shari’ar wacce aka yi, ‘yan sandan sun bayyana cewa beraye sun lamushe kayan shaye-shaye masu nauyin 386kg.
Chaudhary ya sanar da kotu yadda aka ajiye wiwi mai nauyin 700kg kuma duk beraye su ka dinga shanye ta.
Ya ce ‘yan sanda ba su da kwarewa da za su yaki beraye saboda kananun dabbobi ne kuma ba sa tsoron kowa.
A hanyar kai shi kotu, matashi yayi yunkurin lamushe tabar Wiwin da aka kama shi da ita
Wani matashi da aka kama dumu-dumu da tabar wiwi da sauran kayan maye ya yi yunkurin cinye ragowar kayan mayen da ya boye a jikinsa.
Kamar yadda wakilin Dala FM ya bayyana, bayan jami’an tsaro sun kama matashin, sun kwace kayan maye da dama a hannunsa sai dai basu riga sun caje shi ba.
Yana hannunsu yayin da su ke kokarin kai shi caji ofis inda za su tabbatar sun gama caje komai da ke jikinsa ne ya gano cewa zai iya shiga babbar matsala idan su ka gane akwai sauran kayan maye a tare da shi.
Ganin hakan ne yayi kokarin kwaso su inda ya tura baki don yayi sauri ya hadiye su ba tare da kowa ya gane ba, sai dai kash jami’an tsaron sun ankare.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com