Wata mata cikin masu gudanar da umra ta haihu a masallacin ma’aiki dake Madinah wacce ta samu taimakon wasu daga cikin masu yima masallacin ma’aiki Sallallahu alaihi Wasallam hidima.
Daraktan kula da masu yima masallatai hidima na ƙasar ta Saudiyya Dakta Ahmed bin Ali Al-Zahrani, yace wasu daga cikin mutanen su dake aikin hidima wa masallacin ne suka taimaka ma matar wajen haihuwar bayan da suka lura da halin da take ciki na naƙuda.
Yace ana cikin gudanar da ibadah ne wasu daga cikin mutanen nasu suka fahimci cewa matar ta na cikin matsanancin hali na naƙuda ta yanda ba zai yiwu ace an kaita asibiti ba, kamar yadda majiyar mu ta wallafa.
Ya kuma ƙara da cewa daga nan ne mutanen nasu suka bazama cikin aikin agajin gaggawa tare da haɗin gwuiwar wasu masana lafiya a gurin waɗanda suka taimaka mata ta haihu lafiya tare da cika duk wasu sharuɗɗan aikin lafiya.
Bayan haihuwar ne kuma aka garzaya da matar da kuma jinjirin nata zuwa wani asibiti dake kusa da gurin domin ƙara tabbatar da lafiyar ta da kuma ta abinda ta haifa, sabili da akwai buƙatar duba lafiyar tata.
Al-Zahrani ya kuma ƙara da cewa dama daga cikin mutanen nasu akwai waɗanda suka ƙware wajen gudanar da irin waɗannan ayyukan wanda a haka suka samu nasarar taimaka matar ta haihu.
Daga ƙarshe Al-Zahrani ya bayar da 997 a matsayin lambar da za’a riƙa amfani da ita wajen kiran gaggawa domin kiran motar agajin gaggawa, wanda hakan zai sauƙaƙa ma ma’aikatan wajen iya gano inda mai kiran yake da sauri.
A wani labarin na daban kuma, Aƙalla mutane 11 ne ‘yan gida ɗaya aka tabbatar da sun mutu bayan cin wani abinci da ake zargin yana ɗauke da guba a ƙauyen Ikobi dake ƙaramar hukumar Apa dake jihar Benuwai.
Mazauna garin sunce ana tunanin cewa mutanen waɗanda duk ‘yan zuri’a ɗaya ne sun ci wani abinci ne da yake ɗauke da wasu sinadarai na guba, wanda yayi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin su tare da jikkata wasu.
An bayar da sunayen waɗanda suka mutu sanadin cin abincin da Peace Ochoyoda, Aboyi Ngbede Ochefije, Ochefije Ojo, Maria Ojo, Aipu Ochefije, Mary Ochoyoda, Ehi Abu, Blessing Abu, Ojochono Daniel, Adi Ale, da kuma Favour Edoh.
Majiyar mu ta ƙara da cewar mutane shida daga cikin waɗanda suka ci abincin sun mutu ne a wannan rana da suka ci abincin. Su kuma ragowar mutane biyar ɗin sun mutu ne bayan wasu ‘yan kwanaki.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com