34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

‘Yan gida daya su 11 sun mutu bayan cin wani abinci

Labarai'Yan gida daya su 11 sun mutu bayan cin wani abinci

Aƙalla mutane 11 ne ‘yan gida ɗaya aka tabbatar da sun mutu bayan cin wani abinci da ake zargin yana ɗauke da guba a ƙauyen Ikobi dake ƙaramar hukumar Apa dake jihar Benuwai.

Mazauna garin sunce ana tunanin cewa mutanen waɗanda duk ‘yan zuri’a ɗaya ne sun ci wani abinci ne da yake ɗauke da wasu sinadarai na guba, wanda yayi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin su tare da jikkata wasu, kamar yadda Thisday ta wallafa.

An bayar da sunayen waɗanda  suka mutu sanadin cin abincin da Peace Ochoyoda, Aboyi Ngbede Ochefije, Ochefije Ojo, Maria Ojo, Aipu Ochefije, Mary Ochoyoda, Ehi Abu, Blessing Abu, Ojochono Daniel, Adi Ale, da kuma Favour Edoh.

Majiyar mu ta ƙara da cewar mutane shida daga cikin waɗanda suka ci abincin sun mutu ne a wannan rana da suka ci abincin. Su kuma ragowar mutane biyar ɗin sun mutu ne bayan wasu ‘yan kwanaki.

Wani daga cikin mutanen ƙauyen mai suna Ochoyoda Abu, ya bayyana cewa ya rasa matar shi mai suna Mary, da ‘yan uwan shi mata su biyu; Ehi da Blessing, da kuma ɗiyar shi mai suna Peace.

Dagacin ƙauyen na Ikobi mai suna Farfesa Muhammed Adah, a hirar shi da manema labarai ta wayar tarho ya bayyana cewa wani abu makamancin wannan ya taɓa faruwa a watan Satumba da ya gabata.

Yace sun fara fargabar cewa abincin yana ɗauke da guba ne bayan da mutane biyar na farko suka mutu. Yace ya zuwa yanzu sun gayyato ƙwararrun jami’ai daga ma’aikatar lafiya ta jihar don gudanar da bincike.

Dagacin ya ƙara da cewa har ya zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto basu samu sakamakon gwaje-gwajen.

Majiyar tamu ta ƙara da cewar akwai waɗanda kuma sunci abincin amma basu mutu ba, sai dai an garzaya da wasu daga cikin su zuwa asibiti wanda daga bisani duk aka sallame su.

Sai dai a nata ɓangaren, jami’ar hulɗa da jama’a ta ‘yan sandan jihar ta Benuwai, SP Catherine Anene ta bayyana cewa a rahoton da suka samu, mutane bakwai ne suka mutu a rana ɗaya bayan cin abincin.

Ta ƙara da cewar a ranar 14 ga watan nan da muke ciki akwai wani wanda ya mutu a wannan gida. Wata mata daga cikin ‘yan gidan ta deɓo wani ajiyayyen abinci sannan ta dafa shi inda mutane guda 12 suka ci.

Bayan cin abincin nasu ne duk suka kama rashin lafiyar da tayi sanadiyyar mutuwar guda bakwai daga cikin su a rana ɗaya. Sannan kuma tace an garzaya da ragowar biyar ɗin zuwa asibiti inda daga bisani suka warke kuma aka sallame su.

A wani labarin na daban kuma, kunji cewa

Wani matashi ɗan Najeriya ya shiga kaɗuwa matuƙa bayan gano cewa budurwarsa ta kwashe tsawon wata takwas tana rayuwa a cikin wani kango.

A wani bidiyo da matashin ya sanya a manhajar TikTok, ya bayyana cewa bai taɓa ziyartar gidan su budurwar tasa ba saboda bata son ya kawo mata ziyara.

Ya haɗu da mahaifiyar budurwar ta sa
A cikin kangon, ya haɗu da mahaifiyar budurwar tasa wacce tayi farin cikin ganin sa. A lokacin da kyamarar ta ɗauko budurwar tasa, sai ta kulle fuskarta cike da kunya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe