24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Matashi ya kaɗu bayan gano cewa budurwar sa a kango take rayuwa

LabaraiMatashi ya kaɗu bayan gano cewa budurwar sa a kango take rayuwa

Wata matashi ɗan Najeriya ya shiga kaɗuwa matuƙa bayan gano cewa budurwarsa ta tsawon wata takwas a cikin wani kango take rayuwa.

A wani bidiyo da matashin ya sanya a manhajar TikTok, ya bayyana cewa bai taɓa ziyartar gidan su budurwar tasa ba saboda bata son ya kawo mata ziyara. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Ya haɗu da mahaifiyar budurwar ta sa

A cikin kangon, ya haɗu da mahaifiyar budurwar tasa wacce tayi farin cikin ganin sa. A lokacin da kyamarar ta ɗauko budurwar tasa, sai ta kulle fuskarta cike da kunya.

Matashin ya gano cewa ba ita kaɗai bace a wajen mahaifiyarta sannan kuma dole ta sanya ta bar zuwa makaranta.

Mahaifiyar na sana’a domin samun abinda za su ci

Matashin ya bayyana cewa mahaifiyarta na sana’ar siyar da ƙosai domin samun abinda za su riƙa sanyawa a bakunan su.

Ganin inda suke rayuwa ya sanya matashin jin cewa kunya ta kama shi inda har ya kusa fashewa da kuka.

Kalli bidiyon a nan.

Mutane sun tofa albarkacin bakin su kan bidiyon

Oluwatoyin ya rubuta:

“Oya ka tafi gidan mahaifiyarka amma ka ɓishe da zuwa gidan mahaifiyarta.”

Blessing286 ta rubuta:

“Ka ƙauna ce ta a yadda take sannan ka ƙarfafa mata guiwa tayi aiki tuƙuru domin itace ƴar fari, ka ƙarfafa mata guiwa ta jajirce wajen nema domin ta taimaka wa ƴan’uwanta.”

Gracegold3 ta rubuta:

“Abubuwa sun yi wuya. Ubangiji ya albarkace ku. Nima gidan iyaye na irin wannan ne. Ɗan aje lambar asusun banki domin mama.”

BILLIONZ DNK ya rubuta:

“Fatan nasara ɗan’uwa. Yakamata ka kula da ita. Ina maka addu’ar samun buɗi ɗan’uwa, ta yadda zaka iya kula da su. Ƴan’uwan ka ne.”

Kyau na yayi yawa, ban dace in yi aiki ba, kamata yayi in ci daga ɗangare, budurwa

Wata fitacciyar budurwa ‘yar asalin kasar Canada ta janyo surutai bayan bayyana wa mutane cewa kyawunta ya yi yawa don hakan ba za ta iya aiki ba.

Zukekiyar budurwar ta ce bai dace ace kyakkyawar mace irinta ta dinga tashi tun 6 na safe don shiryawa saboda zuwa aiki ba.

Budurwar wacce ‘yar TikTok ce fitacciyat ta ce gaskiya bata dace da zuwa aiki ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe