LabaraiLabaran DuniyaAn zaɓi mace musulma 'yar majalissar jiha a Amurka

An zaɓi mace musulma ‘yar majalissar jiha a Amurka

-

- Advertisment -spot_img

Nabeela Syed, ‘yar asalin ƙasar Indiya ta kasance mace musulma ta farko da aka zaɓa a matsayin ‘yar majalissar jihar Illinois dake ƙasar Amurka, bayan samun gagarumar nasara akan abokin hamayya ta a zaɓen da ya gabata a ranar Talata, 8 ga watan Nuwamban da muke ciki.

Ita ce mace musulma mafi ƙarancin shekaru a ciki

Majiyar mu ta The Islamic Info ta ruwaito cewa Nabeela ‘yar shekara 23, bayan kasancewar ta mace musulma, haka nan kuma itace mafi ƙarancin shekaru a cikin ‘yan majalissun su 51 da aka zaɓa.

A washe garin zaɓen, wato ranar Laraba ne dai Nabeela ta wallafa saƙo na nuna murnar nasarar da ta yi a shafin ta na tuwita, inda ta nuna farin cikin nasarar ta a yankin da ‘yan Republican suke da ƙarfi duk da kasancewar ta ‘yar Demokrat (Democrats).

Matar ta kuma wallafa a shafin ta na Instagram cewa a lokacin da ta ƙuduri aniyar neman takarar, ta ɗauki salon shiga cikin jama’a don nusar dasu kan mahimmancin dimokuraɗiyya gami da nuna musu muhimmanci samun shugabanci na gari.

Ta kayar da ɗan takarar dake kan kujerar

Nabeela Syed dai ta doke abokin hamayyar ta na Republican wanda shine ɗan majalissa mai ci, mai suna Chris bos da kaso hamsin da biyu (52%) na ƙuri’un da aka kaɗa.

Bisa nasarar da Nabeela ta samu, ta zamto itace mace musulma ta farko da aka zaɓa a yankin na Illinois. Akwai wani namiji ɗan asalin Fasasɗin mai suna Abdelnasser Rashid wanda shima musulmi ne da yayi nasara a zaɓen da ya gabata.

Nabeela dai ta kasance mace musulma mai ƙoƙarin sanya hijabi a koda yaushe. An haife ta a yankin Palatine dake Illinois, kuma tayi karatukanta a jami’ar Kalifoniya a ɓangarorin kimiyyar siyasa da kuma harkokin kasuwanci.

Ance ta kasance mace ‘yar gwagwarmaya ce mai ƙoƙarin ƙwato ma waɗanda aka tauye ‘yancin su a yankin da ta fito. Ta taɓa riƙe shugabar wata ƙungiyar sa kai dake taimaka ma masu ƙananan sana’o’i da shawarwari.

Tayi alƙawarin kula da ɓuƙatun al’umma

A ƙudururrukan yaƙin neman zaɓen ta, Syed tayi alƙawarin maida hankali wajen yin abubuwan da suka jiɓanci hidindimun al’umma, musamman irin samun daidaito, ɓangaren kiwon lafiya, ilimi da kuma ɓangaren haraji.

A wani labarin na daban kuma, kunji Wata matashiyar jarumar fim da ta bayyana cewa babu wani namiji da ya taɓa tunkararta da maganar aure, kuma dama tana ganin cewa har yanzu bata kai munzalin da zata yi aure ba.

Sharon Ifedi jarumar fim ce dai ta kudancin Najeriya wacce ta fara taka leda a harkar wasan kwaikwayo tun a lokacin da take a sakandire. Sai dai tana ganin kamar har yanzu shekarun ta basu kai ba na wanda za’a ce tayi aure.

A wata tattaunawa da jarumar, tace a can baya tayi ƙudurin ta karanci ɓangaren aikin likitanci ne kafin daga bisani kuma ta tsinci kanta a harkar fina-finai.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest news

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su ka lamushe wiwi mai nauyin 200kg bayan sun kwace ta...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama shi sannan a sakaya shi saboda ya lakada mata na...

Wata mata ta haihu a masallacin Annabi

Wata mata cikin masu gudanar da umra ta haihu a masallacin ma'aiki dake Madinah wacce ta samu taimakon wasu...

‘Yan gida daya su 11 sun mutu bayan cin wani abinci

Aƙalla mutane 11 ne 'yan gida ɗaya aka tabbatar da sun mutu bayan cin wani abinci da ake zargin...
- Advertisement -spot_imgspot_img

Matashi ya kaɗu bayan gano cewa budurwar sa a kango take rayuwa

Wata matashi ɗan Najeriya ya shiga kaɗuwa matuƙa bayan gano cewa budurwarsa ta tsawon wata takwas a cikin wani...

Babu namijin da ya taba zuwa min da maganar aure – inji Jaruma

Wata matashiyar jarumar fim ta bayyana cewa babu wani namiji da ya taɓa tunkararta da maganar aure, kuma dama...

Must read

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama...
- Advertisement -spot_imgspot_img

You might also likeRELATED
Recommended to you