LabaraiNishadiBabu namijin da ya taba zuwa min da maganar...

Babu namijin da ya taba zuwa min da maganar aure – inji Jaruma

-

- Advertisment -spot_img

Wata matashiyar jarumar fim ta bayyana cewa babu wani namiji da ya taɓa tunkararta da maganar aure, kuma dama tana ganin cewa har yanzu bata kai munzalin da zata yi aure ba.

Jarumar tana Sakandire ta fara harkar fim

Sharon Ifedi jarumar fim ce dai ta kudancin Najeriya wacce ta fara taka leda a harkar wasan kwaikwayo tun a lokacin da take a sakandire. Sai dai tana ganin kamar har yanzu shekarun ta basu kai ba na wanda za’a ce tayi aure.

A wata tattaunawa da majiyar mu ta samu, jarumar tace a can baya tayi ƙudurin ta karanci ɓangaren aikin likitanci ne kafin daga bisani kuma ta tsinci kanta a harkar fina-finai.

Da aka tambaye ta ko an taɓa yi mata tayin aure ba ta amsa ba a waɗannan shekarun nata? Jarumar ta bayyana cewa bata taɓa ba, sabili da a cewar ta babu wani wanda ya taɓa tunkararta da maganar cewa yana son ya aure ta.

Tafi maida hankali kan harkokin fim

Jarumar ta ƙara da cewar dangane da kuma irin namijin da take so, wannan idan lokacin da take ganin ta isa aure yayi zata duba ta gani, tunda a yanzu dai bata san komai ba dangane ga maza.

Ta kuma ƙara da cewar yanzu tafi maida hankali kan sana’ar ta ta fim. Bata alaƙa ko soyayya da kowa. Duk da dai ta tabbatar da cewa akwai mazaje da dama da suke son ta.

Da aka tambayi jarumar kan ko wane irin ƙalubale ne take fuskanta a harkokin ta na wasan kwaikwayo a matsayin ta na jaruma mai ƙaranci shekaru. Jarumar ta bayyana cewa abinda ke takura mata shine, yanayin yadda take baro ‘yan uwanta a gida tun da sassafe ta tafi wajen ɗaukar fim, ba zata dawo ba a wasu lokutan ma sai dare.

Sai dai tace babban ƙalubalen da a yanzu take fuskanta sune sauran matakan da bata taɓa fitowa ba a cikin finafinan da take yi. Tace a matsayin jaruma yana dakyau ace mutum ya iya fitowa a matakai da dama.

Wani ya taɓa rungume ta a tsakiyar jama’a

Ta bayyana cewa wani abu kuma da yakan ɓata mata rai shine yadda wasu daga cikin masoyanta ke yi mata a yayin da suka ganta. Tace akwai lokacin da wani daga cikin masoyanta ya taɓa zuwa ya rungume ta a wajen wani taro da har sai da mutane suka janye shi daga jikin ta.

Daga ƙarshe ta bawa jarumai mata masu tasowa shawara kan su riƙa ƙoƙarin baiwa kansu atisayen fitowa a fim kafin ma suje gaban furodusa. Tace hakan zai taimaka musu sosai.

A wani labarin na daban kuma, kunji Yadda wata matashiyar mata ta kashe ɗan cikin ta da ta haifa.

Wata mata ‘yar shekara 18 dake yankin Olocha-Adogba da ke ƙaramar hukumar Awgu ta kashe ɗan jaririn da ta haifa ta hanyar soka masa wuƙa da tayi.

Majiyar mu ya premium times ta wallafa cewa matar mai suna Joy Okonkwo tayi amfani da wuƙa ne wajen caka ma jaririn nata jim kaɗan bayan haihuwar shi a gida. Mummunan lamarin dai ya faru ne a ranar Litinin data gabata da misalin ƙarfe ɗaya na rana.

Ance wannan ɗanyan aiki dai da ta aikata ya samo asali ne dai daga shawarar da ake tunanin mahaifiyar matar ‘yar shekara 60 mai suna Christiana Okonkwo ta bata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest news

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su ka lamushe wiwi mai nauyin 200kg bayan sun kwace ta...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama shi sannan a sakaya shi saboda ya lakada mata na...

Wata mata ta haihu a masallacin Annabi

Wata mata cikin masu gudanar da umra ta haihu a masallacin ma'aiki dake Madinah wacce ta samu taimakon wasu...

‘Yan gida daya su 11 sun mutu bayan cin wani abinci

Aƙalla mutane 11 ne 'yan gida ɗaya aka tabbatar da sun mutu bayan cin wani abinci da ake zargin...
- Advertisement -spot_imgspot_img

Matashi ya kaɗu bayan gano cewa budurwar sa a kango take rayuwa

Wata matashi ɗan Najeriya ya shiga kaɗuwa matuƙa bayan gano cewa budurwarsa ta tsawon wata takwas a cikin wani...

An zaɓi mace musulma ‘yar majalissar jiha a Amurka

Nabeela Syed, 'yar asalin ƙasar Indiya ta kasance mace musulma ta farko da aka zaɓa a matsayin 'yar majalissar...

Must read

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama...
- Advertisement -spot_imgspot_img

You might also likeRELATED
Recommended to you