Wata mata ‘yar shekara 18 dake yankin Olocha-Adogba da ke ƙaramar hukumar Awgu ta kashe ɗan jaririn da ta haifa ta hanyar soka masa wuƙa da tayi.
Matar tayi amfani da wuƙa wajen kashe yaron
Majiyar mu ya premium times ta wallafa cewa matar mai suna Joy Okonkwo tayi amfani da wuƙa ne wajen caka ma jaririn nata jim kaɗan bayan haihuwar shi a gida. Mummunan lamarin dai ya faru ne a ranar Litinin data gabata da misalin ƙarfe ɗaya na rana.
Ance wannan ɗanyan aiki dai da ta aikata ya samo asali ne dai daga shawarar da ake tunanin mahaifiyar matar ‘yar shekara 60 mai suna Christiana Okonkwo ta bata.
An kai jaririn asibiti
Mai magana da yawun hukumar’yan sanda na jihar ta Enugu Daniel Ndukwe ne dai ya sanar da haka ga manema labarai a hirar da yayi da su a rana juma’a.
Ndukwe yace bayan da matar ta caka ma jaririn nata wuƙa ne aka yi ƙoƙarin yin gaggawar kaishi asibiti inda anan ne likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu.
Ya ƙara da cewa an ajiye gawar gidan adana gawa domin yin binciken ƙwaƙƙwafi. Sannan kuma ‘yan sanda sun kama mutane biyu dangane da hakan.
‘Yan sanda zasu gudanar da bincike
Ya kuma ce Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Enugu Ahmed Ammani ya umarci sashen binciken manyan laifuka na jihar da ya gudanar da bincike tare da hukunta duk waɗanda aka samu da laifi.
Haka nan ya buƙaci mazauna yankin da su kasance masu bin doka da oda, su guji yin duk wani abu da suka san zai iya kawo tarnaƙi a tsakanin al’umma.
Ya kuma buƙatace su da su bawa jami’an tsaron haɗin kai inda ya tabbatar musu da cewar za’a hukunta duk waɗanda aka samu da laifi a cikin lamarin.
Masu laifin dai zasu iya fuskantar hukuncin kisa idan dai aka same su da laifi kamar dai yadda shashi na 319 na kundin hukuncin laifuka na ƙasa ya tanada.
A wani labarin na daban kuma, kunji yadda matashin da yafi Ɗangote kuɗi wata 8 nan baya ya talauce.
Sam Bankman-Fried, matashi ne ɗan shekara 30 wanda watanni 8 da suka wuce nan baya yafi Ɗangote kuɗi, amma kuma yanzu ya koma talaka futuk.
A watanni 8 da suka gabata, matashin wato Sam Bankman yana da dukiyar da yawanta yakai aƙalla dalar Amurka 26, kwatankwacin Naira tiriliyon sha ɗaya da ɗigo huɗu (N11.4 tr) a kuɗin Najeriya, sai dai kuma yanzu bashi da komi na daga wannan dukiya.
Wannan asara dai da Bankman yayi ance itace babbar asara da ake ganin mutum ɗaya ya taɓa yinta a tashi ɗaya a tarihin asarorin da aka yi a duniya.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com