24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Yadda matashin da yafi Ɗangote kuɗi wata 8 nan baya ya talauce

LabaraiLabaran DuniyaYadda matashin da yafi Ɗangote kuɗi wata 8 nan baya ya talauce

Sam Bankman-Fried, matashi ne ɗan shekara 30 wanda watanni 8 da suka wuce nan baya yafi Ɗangote kuɗi, amma kuma yanzu ya koma talaka futuk.

Ya tara sama da tiriliyon sha ɗaya

A watanni 8 da suka gabata, matashin wato Sam Bankman yana da dukiyar da yawanta yakai aƙalla dalar Amurka 26, kwatankwacin Naira tiriliyon sha ɗaya da ɗigo huɗu (N11.4 tr) a kuɗin Najeriya, sai dai kuma yanzu bashi da komi na daga wannan dukiya.

Wannan asara dai da Bankman yayi ance itace babbar asara da ake ganin mutum ɗaya ya taɓa yinta a tashi ɗaya a tarihin asarorin da aka yi a duniya.

Ta ina matashin ya tara wannan dukiyar haka?

Sam Bankman-Fried dai matashi ne ɗan harkar sanannun kuɗaɗen nan na lantarki wato harkar kirifto. A watan Mayu ɗaya gabata, shafin Bloomberg ya sanya matashin a saman Ɗangote a jerin masu kuɗin lokacin.

Shine ke da mallakin kamfanin siye da siyarwar kadarorin kirifto mai suna FTX. Shafin ƙididdige masu kuɗi da yawan dukiyar su na Forbes ya ayyana Bankman a matsayin ‘ƙwararren masanin kirifto’.

A yanzu matashin, wato Bankman-Fried bashi da ko sisi, biyo bayan talauce wa da kamfanin nashi yayi, wanda a sanadiyyar hakan ma an cire sunan shi daga shafin Forbes da Bloomberg.

A wasu ‘yan watanni da suka wuce nan baya, matashin yana cikin masu kuɗi da suka yi fice a duniya. Haka nan ma kamfanin na shi na FTX yana daga cikin waɗanda suka shahara, amma sai gashi yanzu an wayi gari bashi da ko sisi.

Karyewar kasuwar ce ta janyo mishi asara

A ‘yan watannin da suka shuɗe, kasuwar ta kirifto ta fuskanci ƙalubale iri daban-daban waɗanda suka janyo ma mutane da dama munanan asarori na maƙudan kuɗaɗen da suka zamto sanadiyyar talaucewar wasu daga cikin fitattun masu yin harkar.

Matashin yayi rubutu a shafin shi na tuwita inda ya nuna matuƙar mamakin shi bisa yadda wannan abu ya faru haka.

Mutane da dama dai na ta bayyana irin gagarumar asarar ɗumbin dukiya da suka tafka sakamakon rashin daidaituwar kasuwar ta kirifto.

A wani labarin na daban kuma, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi kira ga ‘yan ƙasa da su zaɓi duk wanda yayi musu ko a wacce jam’iyya yake.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ɗaukacin ‘yan Najeriya akan su zaɓi duk wani wanda suka ga dama ba tare da la’akari da jam’iyyar da ya fito ba a kakar zaɓen 2023 da ke ta ƙaratowa.

Buhari ya kuma ce ba zasu bari wani yazo ya ɗebo kayayyaki ko kuma ‘yan daba don a tsorata ko hana mutane yin zaɓe a duka mazaɓu.

Majiyar mu tace shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a  ziyarar da ya kai a ƙasar Birtaniya jim kaɗan bayan kammala wani taro da sarkin Ingila, wato Sarki Charles na uku.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe