24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Kace ka fasa auren kawai: Yadda ango ya isa wurin ɗaurin aurensa a akwatin gawa

LabaraiKace ka fasa auren kawai: Yadda ango ya isa wurin ɗaurin aurensa a akwatin gawa

Wani mutum ya wallafa bidiyon wani ango cikin akwatin gawa yayin da ya isa wurin daurin aurensa wanda hakan ya yi matukar daukar hankula, Legit.ng ta ruwaito.

Mutane da dama sun yi zargin kawai angon ba ya don a daura auren ne, hakan yasa zai mayar da shagalin tamkar zaman makoki.

A gajeren bidiyon wanda @tobz88 ta wallafa a shafinta na TikTok an ga inda aka kawo ango wurin daurin aurensa cikin akwatin gawa.

Yayin da kyakkyawar amaryarsa ke jiran iso isowarsa tare da abokansa, wannan lamari ya yi matukar ba su mamaki.

Bayan sauke akwatin gawar a bayan amaryar, an bude shi inda aka ga angon ya yi gaggawar fitowa.

An yi shagalin auren ne a bakin ruwa wanda wasu bakin da su ka halarci daurin auren su ka fitar da wayoyinsu su na daukar hotuna da bidiyoyi.

Mutane da dama sun sha mamakin wannan lamari inda wasu ke cewa da su na wurin ba za su tsaya ba, wucewa kawai za su yi saboda takaici.

Magidanci ya cinnawa ƴaƴan matarsa wuta bayan ta ƙi yarda su yi kwanciyar aure

Wani magidanci ya cinnawa ƴaƴan matar sa guda biyar wuta bayan ta hana shi su yi kwanciyar aure.

Magidancin mai suna Ojo Joseph mai shekara 54 a duniya ya aikata wannan aika-aikar ne a jihar Ondo.

Lamarin ya auku ne a unguwar Fagun cikin garin Ondo a ranar Lahadi 6 ga watan Oktoɓan 2022 da safe. Majiyar mu ta jaridar The Cable ta rahoto.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe