36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Dakarun sojojin Najeriya sun halaka wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga

LabaraiDakarun sojojin Najeriya sun halaka wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga

Bayan kwashe dogon lokaci yana addabar mutane da tserewa jami’an tsaro, wani ƙasurgumin shugaban ƴan ta’adda mai suna ‘Dogo Maikasuwa’ ya gamu da ajalin sa a hannun dakarun sojojin Najeriya.

Wata sanarwa da kwamishin tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar ta tabbatar da aukuwar lamarin. Jaridar Daily Nigerian ta rahoto.

Ya daɗe yana addabar mutanen yankin

“Bincike ya nuna irin ta’asar da ya riƙa gudanarwa inda yake cin karen sa ba babbaka a wurare masu wahalar zuwa.”

Dogo Maikasuwa, wanda kuma ake kira da ‘Dogo Maimillion’ ya jagoranci hare-hare da dama akan mutanen dake bin titin hanyar Kaduna-Kachia, da kuma ƙauyukan dake tsakanin ƙananan hukumomin Chikun da Kajuru. Yana ɗaya daga hatsabiban ƴan bindiga da suka addabi yankin.

A lokacin da yake gab da sheƙawa barzahu, Dogo MaiKasuwa, tare da mayaƙan su sun afkawa wani kwanton ɓauna da dakarun sojojin suka yi musu a cikin daji a yankin Gengere-Kaso tsakanin iyakokin Chikun da Kajuru.

Dakarun sojojin sun yi ƙazamin bata kashi da ƴan bindigan

“Jami’an tsaron bayan anyi ƙazamin bata kashi sun samu nasarar halaka shugaban ƴan bindigan sannan suka kwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, harsasai biyar, babura biyu da kayan sojoji kala ɗaya.”

“Sauran ƴan bindiga sun arce ɗauke da raunikan bindiga. An kuma samu cewa daga baya ɗaya daga cikin su ya mutu inda sauran suka tafi da gawar.” A cewar Aruwan.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yabawa jami’an tsaron bisa bajintar da suka nuna a fafatawar su da ƴan bindigan.

Kaduna: Dakarun sojoji sun lalata sansanin ƴan bindiga 100, sun tura da dama barzahu

Dakarun sojojin Najeriya sun halaka ƴan bindiga 152 sannan sun lalata sama da sansanin su guda 100 a jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, shine ya bayyana hakan inda yace sojojin sun samu wannan nasarar ne a tsakiya da ƙarshen shekarar 2022.

Ya dai bayyana hakan ne a yayin da yake bayar da rahoton yanayin tsaro na tsakiya da ƙarshen shekarar 2022 ga gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe