People’s Magazine ta nada wani jarumin finafinan Amurka, Chris Evans, a matsayin namiji mai rai mafi daukar hankali a shekarar 2022, The Punch ta ruwaito.
An bayar da wannan sanarwar ne a wani shirin dare da aka yi a Stephen Colbert wanda aka haska ranar Litinin.
Shafin mujallar ma ya bayyana hotunan Evans a gabanshi tare da bayyana wannan babban matsayi wanda tauraron ya samu a ranar Juma’a.
Tauraron fim din Captain America ya shiga jerin su Idris Elba, George Clooney, Brad Pitt, Michael Jordan, Chris Hemswortha da sauransu wadanda su ka rike wannan matsayi.
Evans zai amshe wannan mukamin a hannun Paul Rudd wanda aka nada a wannan mukamin a Nuwamban 2021z Evans mai shekaru 41 ya bayyana cewa mahaifiyarsa za ta yi matukar farinciki idan ta samu wannan labarin yayin da abokansa ke ta zolayarsa.
Kamar yadda yace:
“Mahaifiya ta za ta ni dadi kuma za ta yi alfahari da hakan. Wannan zai ja min zaulaya. Amma ina daidai da wadanda za su min.”
Ya ce yana matukar kulawa da lafiyarsa yayin da yake kara shekaru. A baya yana cin komai amma yanzu ya fara kiyayewa.
Ya ce wannan nadi da aka yi masa abu ne da zai tuna idan ya tsufa ya sauya kamanni.
Jerin ƙasashe huɗu inda mace ke auren fiye da namiji ɗaya
baƙon abu bane jin cewa maza na auren mace fige da ɗaya, inda al’adu da addinai dama a duniya na goyon bayan wannan ɗabi’ar. Sai dai abin akwai ban mamaki jin cewa mace ta auri namiji fiye da ɗaya.
Ga jerin ƙasashen da mata ke auren namiji fiye da ɗaya wanda jaridar Tribune.ng ta tattaro.
Indiya
Ɗaya daga cikin ƙasashen da suka amince mace ta auri namiji fiye da ɗaya itace Indiya. Akwai ƙabilu da dama a ƙasar dake wannan ɗabi’ar. An dai fi samu a sassan Arewacin ƙasar a irin su Paharis na yankin Jaunsarbawar, yayin da a Kinnaur, Himachal mutane tsiraru sun yarda suna yi.
A matsayin su na tsatson Pachi Pandavas, sun yi amanna cewa yakamata su cigaba da wannan al’adar. Haka kuma a sassan Kudancin Indiya akwai ƙabilu irin su Toda a Nilgris, Najanad Vellala a Travancore, da wasu a ƙabilar Nair da suke yin wannan ɗabi’ar.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com