Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna yatsa ga ƙasashen Yammacin duniya kan rashin ɗaukar matakan da suka dace domin daƙile matsalar sauyin yanayi.
Shugaba Buhari ya kira ƙasashen na Yamma da ‘munafukai” saboda gazawarsu wajen ɗaukar matakan da suka dace kan matsalar sauyin yanayi da duniya ke fama da ita.
Buhari ya nuna gazawar ƙasashen Turai wajen ɗaukar matakan da suka dace
Jaridar BBC Hausa ta ambato shugaba Buhari na cewa:
“Da yawa daga cikin takwarorina (shugabannin ƙasa) na nuna damuwa game da munafurcin ƙasashen Yamma da gazawarsu wajen kasa ɗaukar matakin da ya dace.”
Shugaba Buhari ya jaddada cewa shugabannin Turai sun sha nuna gazawar su wajen cika alƙawarin su na samar da dala biliyan 100 ($100bn) domin kawo ƙarshen “matsalar sauyin yanayi da suka haifar da kansu” ga ƙananan ƙasashe masu tasowa.
Yayi wani muhimmin gargaɗi ga ƙasashen Turai
Shugaba Buhari ya kuma ƙara da cewa daga yanzu ba zai yiwu ƙasashen na Turai su riƙa tsarawa ƙasashen Afirka yadda ya kamata su yi amfani da ma’adanan da suke da su ba.
“Kar ku faɗa wa ‘yan Afirka yadda ya kamata su yi amfani da arzikinsu. Da a ce Afirka za ta yi amfani da dukkan arzikin iskar gas da take da shi a rumbuna, wanda shi ne mafi inganci ga muhalli, hayaƙin da ke gurɓata yanayin duniya zai tashi daga kaso 3 cikin 100 zuwa kaso 3.5.”
Afirka na fitar da kashi kusan uku ne kacal na hayaƙi mai gurɓata muhalli a gabaɗaya duniya amma tana cikin nahiyoyin da suka fi kowace fuskantar bala’in haɗarin sauyin yanayin.
Ku zaɓi duk wanda yayi muku ko a wacce jam’iyya yake – Buhari
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ɗaukacin ‘yan Najeriya akan su zaɓi duk wani wanda suka ga dama ba tare da la’akari da jam’iyyar da ya fito ba a kakar zaɓen 2023 da ke ta ƙaratowa.
Buhari ya kuma ce ba zasu bari wani yazo ya ɗebo kayayyaki ko kuma ‘yan daba don a tsorata ko hana mutane yin zaɓe a duka mazaɓu,
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com