Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ɗaukacin ‘yan Najeriya akan su zaɓi duk wani wanda suka ga dama ba tare da la’akari da jam’iyyar da ya fito ba a kakar zaɓen 2023 da ke ta ƙaratowa.
Ba zamu bari a razana mutane da ‘yan daba ba
Buhari ya kuma ce ba zasu bari wani yazo ya ɗebo kayayyaki ko kuma ‘yan daba don a tsorata ko hana mutane yin zaɓe a duka mazaɓu, kamar yadda jaridar Dailytrust ta wallafa.
Majiyar mu tace shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a ziyarar da ya kai a ƙasar Birtaniya jim kaɗan bayan kammala wani taro da sarkin Ingila, wato Sarki Charles na uku.
Buhari yace yana son ‘yan Najeriya su gamsu cewa gwamnatin sa ta damu da damuwarsa. kuma yana so ya zambo an sami abinda za’a riƙa tunawa da shi ko bayan mulkin shi.
Ya kuma bayyana ƙwarin gwuiwa inda yake ganin cewa ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar su wato Bola Ahmed Tinubu zai yi nasara zaɓe mai zuwa.
APC tayi nasara da samu Tinubu
Kamar yadda Buhari ya bayyana, yace jam’iyyar APC tayi gagarumar nasara da tsayar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugabancin ta. Da aka tambaye shi kan ko yaya yake kallon jam’iyyar a zaɓe mai zuwa, Buhari yace APC zata yi nasara a zaɓen.
Ya ce a matsayin Tinubu na sanannen ɗan siyasa kuma tsohon gwamnan jihar Legas, jihar da tafi kowacce yawan arziki da kuma yawan maziyarta, Buhari ya ce ba ƙaramar Smsa’a jam’iyyar tasu ta APC tayi ba.
Da yake ƙara jawabi dangane da ziyarar, shugaba Buhari yace ziyarar shi zuwa ga sarki Charles na uku domin ƙara ƙulla alaƙa ne tsakanin ƙasashen guda biyu.
Ya kuma ƙara da cewar sarkin na Birtaniya na matuƙar son ƙulla alaƙa da Najeriya. Ta yiwu ƙila saboda daɗaɗɗiyar alaƙar da ta kasance tsakanin Najeriya da kuma ƙasar ta Birtaniya.
Buhari yace ba shi da gida a Birtaniya
Sarki Charles ya tambayi Buhari akan ko yana da gida a ƙasar ta Birtaniya, ya kada baki yace ma sarki Charles cewa shi bai shi da gida a nan Birtaniya. Buhari yace tunda ya hau kan karagar mulki bai mallaki ko gida ɗaya ba a Ingila. Yace shi baya da ra’ayin mallakar gidaje a gurare daban-daban.
A wani labarin na daban kuma, kunji yadda wani lauya ya kai ƙarar Asadussunnah da Mahdi Shehu wajen jami’an farin kaya.
Wani ƙwararren masanin shariah mai zaman kanshi mai suna Abbas Mu’azu ya kai ƙarar Asadussunnah, fitaccen malamin addinin musulunci da kuma mai rajin kare haƙƙin ɗan adam kuma ɗan kasuwa Mahdi Shehu zuwa ga jami’an tsaron farin kaya.
Lauyan ya bayyana cewa dalilin shi na shigar da malamin da kuma ɗan kasuwar ƙara ya ta’alaƙa ne dai da yadda suke kalaman da a cewar shi zasu iya kawo hargitsi musamman ma dai duba da yadda ake tunkarar zaɓen 2023.