Hukumar ƴan sandan jihar Legas ta bazama neman wani magidanci ruwa a jallo bayan ya cinnawa matarsa wuta.
Magidancin mai suna Akpos ana zarginsa da cinnawa matarsa mai suna Risikat, wuta wacce tayi sanadiyyar rasuwarta a mazaunin su dake kan titin Ayide Osolo, Divine Estate, a yankin Ijanikin na jihar Legas. Shafin LIB ya rahoto.
Lamarin ya auku ne a gidan ma’auratan
Shaidun gani da cewa sun tabbatar cewa Akpos da Risikat suna tare a cikin gidansu lokacin da rigima ta ɓarke a tsakanin su.
Rigimar tayi ta ruruwa wanda har ya kai ga Akpos ya ɗauko jarkar man fetur ɗin su ya ƙwararawa matar sa sannan ya banka mata wuta.
Bayan ya fahimci girman aika-aikar da ya tafka, sai magidancin ya ranta a na kare wanda har yanzu ba a san inda yake ba
Makwabta sun garzaya da Risikat zuwa wani asibiti mafi kusa da su inda daga bisani ta rasu yayin da ake duba lafiyarta bisa ƙunannakin data samu.
Ƴan sanda na neman magidancin ruwa a jallo
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin hukumar ƴan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa:
“An shigar da wani ƙorafi a ofishin ƴan sanda na Ijanikin cewa wata mata mai suna Risikat, mai shekara 48 a duniya, sun yi rigima da mijinta wanda suna cikin rigimar ya ƙwarara mata man fetur sannan ya cinna mata wuta.”
“Lamarin ya sanya ta samu munanan raunikan ƙuna sannan an garzaya da ita zuwa asibiti domin duba lafiyarta amma ta rasu. Ana ƙoƙarin ganin an cafko wanda ake zargin tun bayan tserewar sa.”
Magidanci ya cinnawa ƴaƴan matarsa wuta bayan ta ƙi yarda su yi kwanciyar aure
Wani magidanci ya cinnawa ƴaƴan matar sa guda biyar wuta bayan ta hana shi su yi kwanciyar aure.
Magidancin mai suna Ojo Joseph mai shekara 54 a duniya ya aikata wannan aika-aikar ne a jihar Ondo.
Lamarin ya auku ne a unguwar Fagun cikin garin Ondo a ranar Lahadi 6 ga watan Oktoɓan 2022 da safe.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com