24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Lauya ya kai ƙarar Asadussunnah da Mahdi Shehu

LabaraiSiyasaLauya ya kai ƙarar Asadussunnah da Mahdi Shehu

Wani ƙwararren masanin shariah mai zaman kanshi mai suna Abbas Mu’azu ya kai ƙarar Asadussunnah, fitaccen malamin addinin musulunci da kuma mai rajin kare haƙƙin ɗan adam kuma ɗan kasuwa Mahdi Shehu zuwa ga jami’an tsaron farin kaya.

Yace suna yin kalaman ɓatanci

Lauyan ya bayyana cewa dalilin shi na shigar da malamin da kuma ɗan kasuwar ƙara ya ta’alaƙa ne dai da yadda suke kalaman da a cewar shi zasu iya kawo hargitsi musamman ma dai duba da yadda ake tunkarar zaɓen 2023.

A takardar shigar da ƙarar wacce ya aika ma shugaban hukumar jami’an tsaro na farin kaya DSS, Shugaban hukumar zaɓe na ƙasa da kuma gidan jaridar Leadership. Ya bayyana cewa babu abinda Sheikh Yusuf Asadussunnah da kuma Mahdi Shehu suke yi face kamfen na ɓatanci da kuma nuna ƙabilanci.

Kalaman su zasu iya janyo hargitsi

Ya ƙara da cewa abubuwan da Asadussunnah da Mahdi ke yi ba wai iya dokokin zaɓe yake karya wa ba, yace abu ne da zai iya kawo hargitsi a cikin ƙasar.

A cikin wasiƙar tashi, ya ce abubuwan da Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah da kuma Mahdi Shehu keyi abubuwa ne da ba Allah a ciki. Ya ce yayi bayani gamsasshe a cikin takardar koken kan yadda zasu ayyukan nasu ka iya tada rikici kafin, ko zuwa zaɓen 2023.

Yace Asadussunnah yana amfani da kujerar shi ta malunta wajen ƙoƙarin bata sunan ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu domin sanya ‘yan Arewa ƙin zaɓar shi a kakar zaɓe mai zuwa.

Asadussunnah yana ɓata Tinubu ya na ma Atiku kamfen

Ya ƙara da cewa daga cikin maganganun da malamin yayi akwai maganar cewa wai ina Tinubu ya ci zaɓe zai maida babban birnin tarayya daga Abuja zuwa Lagos wanda yace wannan ba gaskiya bane. Sannan kuma malamin yayi amfani da haka wajen yima ɗan takarar shugabancin ƙasa na PDP Atiku Abubakar kamfen.

A wani labarin na daban kuma, kunji wani agola ya kashe mijin mahaifiyar shi wajen gwajin maganin bindiga.

Wani yaro ya kashe mijin mahaifiyar shi a yayin da suke gwajin maganin bindiga. Lamarin dai ya faru ne a ranar Lahadin data gabata, 6 ga watan Nuwamban da muke ciki a ƙaramar hukumar Jada dake jihar Adamawa.

Mutumin wanda aka bayyana sunan shi da Yusuf ya rasa ransa ne bayan da ya umarci ɗan-ɗan matar shi wato agolan shi akan ya harbe shi da wata bindiga da ya bashi domin ya gwada ƙarfin wani maganin bindiga da ya sha, kamar dai yadda majiyar mu ta wallafa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe