Wata mata mai ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki (HIV) watau ƙanjamau ta bayyana cewa ta haɗa jininta da zoɓon da take siyawar domin ta sanya wasu mutanen su kamu da cutar.
Matar ta bayyana hakan a wani shirin gidan rediyon Wazobia FM mai suna MarketRunz a daren ranar Laraba. Jaridar The Punch ta rahoto.
Mai gabatar da shirin ya nemi masu sauraro da su kira waya su bayyana abinda suka yi a kasuwa wanda mutane basu sani ba wanda kuma ba su ji daɗin aiwatarwa ba.
Matar ta bayyana dalilin da ya sanya aikata wannan ɗanyen aikin
Matar mai siyar da zoɓon ta bayyana cewa:
“Naje asibiti wata shida da suka wuce inda aka gayamin ina ɗauke da cutar ƙanjamau.”
“Na fara sanya jini na cikin zoɓon da nake yi na siyarwa sannan na siyarwa da mutane da dama.”
“Na ɗebi jinina da sirinji sannan na haɗa shi da zoɓo. Da ni ma’aikaciyar jinya ce amma bayan an tabbatar ina ɗauke da cutar ƙanjamau dole na bar aikin.”
“Ban ji daɗin abinda na aikata ba amma naji daɗi ba zan mutu ni kaɗai ba.”
“Yanzu na kai wata shida ina yin wannan taɓargazar sannan jna fatan ubangiji zai yafe min.”
Sai dai, binciken da jaridar The Punch tayi, ta gano cewa ba’a ɗaukar cutar ƙanjamau ta hanyar ruwa ko abinci.
Ba a ɗaukar cutar ƙanjamau ta hanyar abinci ko abin sha
Jaridar ta ambato ƙungiyar lafiya ta duniya (WHO) na cewa:
“Ba’a ɗaukar cutar ƙanjamau ta hanyar abinci ko abu mai ruwa. Tabbas zata iya rayuwa a wajen jikin mutum na tsawon minti ɗaya.”
Yanzu haka na shafa wa maza 119 da mata 19 cutar kanjamau, inji budurwar da ta kamu da cutar a 2016
Wata budurwa ‘yar Najeriya ta bayyana yawan mutanen da ta shafawa cutar kanjamau, bayan an tabbatar da tana dauke da cutar a shekarar 2016, LIB ta ruwaito.
‘Yar Najeriyar mai amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ta bayyana yadda a yanzu haka ta shafa wa kimanin maza 115 da mata 19, sannan tana cigaba da kirga.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com