Musulmai da mabiya addinin Hindu sun nuna kan su a haɗe yake a cikin ƴan kwanakinnan a garin Ramgarh, gundumar Alwar a jihar Rajasthaɓ ta ƙasar Indiya.
Hakan ya bayyana ne lokacin da shugaban kwamitin ilmi na Anjuman da shugaban Panchayat, Samiri Nasru Khan, suka haɗa hannu wajen aurar da wata marainiyar ƴar addinin Hindu. Jaridar The Islamic Information ta rahoto.
Ƴan kwamitin suka zama kawunnan amarya a wajen bikin
Musulman da suka fito daga waɗannan ƙauyukan sun zo a matsayin kawun nan amarya domin wani biki na musamman da ake kira Myra ko Bhaat. Sun bayar da tallafi hada na kuɗi wanda ya kai Rs 31,000 da sauran kyaututtuka, sannan suka taimaka aka shirya abinci domin shagalin bikin amaryar.
Amaryar mai suna Aarushi, mazauniyar Ramgarh, ta zama marainiya ne bayan ta rasa iyayenta tana ƴar shekara ɗaya a duniya.
Duk da cewa ta taso ne a gidan marasa ƙarfi, kawunta Jayaprakash Jangid da matar sa sun kula da ita wanda har karatu tayi zuwa matakin MA.
Bayan samun labarin cewa Aarushi zata auri Dalchand, wani mazaunin Dholi Dubh, cikin gaggawa Nasru Khan ya nemi da ya ɗauki nauyin bikin duba da yanayin da iyalanta ke ciki.
Mambobin kwamitin sun ziyarci gidan su Aarushi a ranar Juma’a inda suka taimaka aka aurar da ita cikin cikakkiyar al’adar Hindu.
Ƙungiyar ta Anjuman itace ta ɗauki nauyin dukkanin abinda aka gudanar a wajen bikin sannan ta bayar da wasu kyaututtukan kayan aure ga Aarushi. Bayan kammala bikin an ga Aarushi tana rungumar su.
Ƙungiyar ta saba yin irin waɗannan ayyukan
Ta hanyar tattara kuɗi a tsakanin su, kwamitin yayi suna wajen yin irin waɗannan ayyukan a baya, inda suka taimakawa wasu ƴanmata mabiya addinin Hindu talakawa biyar suka yi aure.
Haka kuma sun shirya aurar da ƴanmata musulmai 560 a tare a baya.
Halaye masu kyau da na koya a wajen Musulmai -Wata budurwa Kirista
Wata budurwa mabiyar addinin kirista ta bayyana wasu muhimman dabi’u da ta koya daga wajen Musulmai.
A cikin wani bidiyo da budurwar mai suna Gayobi Achawa ta saka a shafin TikTok, ta bayyana cewa ita ba Musulma bace amma tana da ‘yan’uwa Musulmai a cikin danginta
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com