36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Wani agola ya kashe mijin mahaifiyar shi wajen gwajin maganin bindiga

LabaraiWani agola ya kashe mijin mahaifiyar shi wajen gwajin maganin bindiga

Mutumin yana gwajin maganin bindiga ne

Wani yaro ya kashe mijin mahaifiyar shi a yayin da suke gwajin maganin bindiga. Lamarin dai ya faru ne a ranar Lahadin data gabata, 6 ga watan Nuwamban da muke ciki a ƙaramar hukumar Jada dake jihar Adamawa.

Mutumin wanda aka bayyana sunan shi da Yusuf ya rasa ransa ne bayan da ya umarci ɗan-ɗan matar shi wato agolan shi akan ya harbe shi da wata bindiga da ya bashi domin ya gwada ƙarfin wani maganin bindiga da ya sha, kamar dai yadda majiyar mu ta wallafa.

Mutumin wanda aka ce ɗan sa kai ne ya ɗaura wasu layu a jikin shi waɗanda ake tunanin na maganin bindiga ne, sannan ya umarci agolan nashi mai suna Adamu akan ya harbe shi da bindigar.

Mutumin baya cikin hayyacin shi

Sai dai wasu sunce Yusuf ɗin ba a cikin hayyacin shi yake a lokacin da ya buƙaci a harbe shi da wannan bindigar. Wasu na ganin cewa kamar ya sha wani abun da ya gusar masa da tunanin sa.

Adamu ya bayyana cewa a lokacin da yake ƙoƙarin komawa gida ne mijin mahaifiyar tashi ya kira shi ya bashi wata bindiga da yayi ma ɗuri inda ya buƙaci ya harbe shi da ita, saboda taƙamar ya ɗaura layu da gurayen maganin bindiga.

Yace da farko yayi gardama amma baban nashi ya matsa akan sai ya harbe shi, inda ya saita bindigar a cikin shi sannan ya umarci da ya harbe shi ba zata kama ba.

Ya matsa a harbe shi da bindigar

Yace duk da haka yaƙi ya harba bindigar, amma ya matsa mishi sai ya harbe shi. Shi kuma domin ya yi mishi biyayya sai ya kawai ya harba inda a nan take bulet ɗin huda shi, kuma yayi mishi mummunan rauni. Take aka dauke shi zuwa asibiti inda a can ne aka tabbatar da ya rasu.

Mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda ta jihar Adamawa ya bayyana cewa duk wanda aka samu da hannu a cikin lamarin za’a hukunta shi.

A wani labarin na daban kuma, kunji yadda wata matashiya ta bayyana cewa ita bata jin ɗaɗin abinda rahama Sadau take yi.

Wata matashiya mai suna Maryamah ta bayyana cewa gaba ɗaya bata jin daɗin abinda jaruma Rahama Sadau take yi na yanda take shiga ta bayyana surar jikin ta.

Ta bayyana hakan ne a wani rubutu da tayi a shafin ta na Tuwita, inda ta nuna cewa ita bata jin daɗin yadda Rahama Sadau ɗin ke yin shigar ta saboda tana matuƙar mutunta ta.

Ta ƙara da cewar matan dake yin ƙoƙari wajen bin dokokin Allah suna matan da suka fi kyawu a cikin wannan duniyar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe