Tsohuwar jarumar Kannywood, Rahama Hassan wacce ta ja zarenta a lokacin tana tsundum a harkar fim, tana gab da kammala digirinta na biyu kamar yadda ta bayyana.
Kamar yadda ta wallafa a shafinta na Instagram tare da wallafa hotonta wanda ta dauka lokacin da ta shiga jami’a don fara karatun digirin na biyu.
Dama ta shigo masana’antar bayan kammala digirinta na farko inda aka dinga haskata a finafinai kamar Zarar Bunu, Birnin Masoya da sauransu.
Bayan nan ne tayi aure wanda tsawon lokaci ba a sake jin duriyarta ba. Sai dai ta bayyana lokacin da ta haifi diyarta wanda aka dinga yi mata sambarka.
Daga bisani kuma an gan ta a taron babbar kungiyar da ke tallafawa jaruman fim ta 13 times 13, da siga mai kama da aurenta ya mutu.
Ya dinga daukar hotuna da jaruman masana’antar tare da wallafa hotuna da jaruman kudu wanda a lokacin da take da aure duk bata yi ba.
A wallafar da tayi karkashin hoton nata ta ce:
“Shagalin shiga makaranta. Na kusa kammala digirina na biyu.”
Wannan ya kara bayar da tabbaci akan cewa aurenta ya mutu. Muna mata fatan alheri, Ubangiji ya sanya alkhairi kuma yasa tsawon rai aka yi wa.
Ga wallafar:
Auren Rahama Hassan ya mutu, ta dawo harkar Kannywood
A bidiyon, wanda Tashar Tsakar Gida ta nuna, an ga tsohuwar jarumar tare da sauran jarumai sanye da hula ta kungiyar mawaka da jarumai ta 13 X 13, inda mai shaddan ya rubuta “Rahama Hassan is back” ma’ana “Rahama Hassan ta dawo”.
Wannan bidiyon ne ya kara bayar da tabbacin cewa auren Rahama Hassan ya mutu saboda babu yadda za ayi da aurenta ta dawo fim har su kai ga yin tsayuwae gab da gab da MaiShadda.
Musamman idan mutum ya kalli yadda jarumar ta dakata da yin fina-finai tun kafin ta yi aure har ta kai ga yin aure.
Ko a shafukan sada zumunta ba a fiye jin ta ba sai jefi-jefi.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com