24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Ina so in yi rayuwa ta har abada, Fitaccen mawaƙin kudu, Wizkid

LabaraiIna so in yi rayuwa ta har abada, Fitaccen mawaƙin kudu, Wizkid

Fitaccen mawakin kudu wanda ya dade ana damawa da shi, Ayodeji Ibrahim Balogun, wanda aka fi sani da Wizkid, ya bayyana burinsa a rayuwa inda yace yana fatan ya kasance kamar Bob Marley, Gistlover.com ta ruwaito.

A wata tattaunawa da aka yi da shi, yayin bayani akan sabon albam dinsa mai zuwa, ‘More Love Less Ego’ wanda ya dace da yadda yake jin kansa ya ce burinsa ya rayu har abada a harkar waka kamar Marley.

Ya ce zai zage damtse har sai ya ga ya yi wakoki hadaddu wadanda za a dinga sanyawa ko bayan ba ya da rai.

Kamar yadda ya shaida:

Ina so in rayu har abada. Ba wai a fili ba, A’a ina so in yi abinda har abada za a dinga tunawa da ni.

A cewar Big Wiz, idan yana kallon wakokin Bob Marley, kawai yana kara kallon abinda yake fatan yi ne a rayuwarsa.

A cewarsa duk da dai ya dade da rasuwa amma ba a manta da shi ba. Ya ci gaba da cewa:

Ban ma san ya rasu yana da shekaru 36 ba ne. Amma ya yi abubuwa da dama yayin da yake da karancin shekaru. Wannan na kara ba ni tabbacin cewa zan iya abinda nake fatan yi.

Saboda na dan watarana za a sanya wakoki na ana tunawa da ni.” Ya ce a ranar 11 ga watan Nuwamban 2022 zai saki sabuwar wakarsa mai suna “More Love Less Ego.

Rahama Sadau ta sake tsunduma fina-finan kudu na Nollywood bayan korarta daga Kannywood

Biyo bayan korar da aka yiwa jaruma Rahama Sadau, tun bayan bayyanar wasu hotuna na tsiraici, inda hakan ya haddasa har takai ga kungiyar Moppan sun kori jarumar daga masana’antar.

Bayan korar ta kungiyar sun kuma nesanta kansu da ita baya ga taron dangin da ‘yan uwanta jarumai suka yi mata wajen yi mata tofin ala tsine.

Baya ga haka mun ga cewa jarumar ta yanke duk wata alaka da manyan jiga-jigan masana’antar ta hanyar daina bin su a shafukan sada zumunta, haka suma sun daina bin ta, haka kuma sun janye al’amuransu daga nata ciki kuwa harda Sarki Ali Nuhu da Adam A Zango.

Sai dai kuma tun lokacin da kura take tsaka da turnukewa jarumar ta fito ta bada hakuri, harda kukanta da kuma nesanta kanta da abin, da kuma daukar laifinta kasancewar ita ce ummul’aba’isin abun da ya faru.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe